Mu yi wa ƴan Najeriya adalci mu kawo musu sauƙi – Tambuwal
Mu yi wa ƴan Najeriya adalci mu kawo musu sauƙi – Tambuwal
Mintuna 5 da suka wuce
Wani jigo a babbar jam'iyyar adawar Najeriya wato PDP, ya ce a ganinsa har yanzu gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba ta ɗauki hanyar gyara ba kan halin matsin rayuwar da ake fama da shi a ƙasar.
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya ce: "Ni a nawa ra'ayi, har yanzu gwamnatin Bola Tinubu, ba ta ma kama hanya ta yadda za ta shawo kan waɗannan matsaloli musamman na tattalin arziƙi na Najeriya ba, ballantana har a ce ta yi nasara".
Ya ce halin da ake ciki a Najeriya, yana buƙatar gwamnati da jagororin siyasa irinsa, su yi wa jama’a adalci a kawo sauƙin rayuwa.
"Mahi yawancin ƴan Najeriya ba su yi tsammanin za su shiga halin da suke ciki yanzu ba."
Yana wannan jawabi ne a wani ɓangare na jerin hirarraki da ƙusoshin siyasar Najeriya, da muke kawo muku, albarkacin cikar mulkin dimokraɗiyyar ƙasar shekara 25 babu katsewa a karon farko na tarihin ƙasar.
Tsohon gwamnan na Sokoto ya ce halin matsin rayuwar da ake fuskanta a ƙasar, wani babban cikas ne ga mulkin dimokraɗiyya.
A cewarsa, mulkin dimokraɗiyya ya kawo ci gaba a Najeriya musamman idan an aka yi la'akari da taka wa wani tsohon shugaban ƙasar burki lokacin da ya yi yunƙurin tazarce a ƙarshen wa'adinsa na biyu.
Ya ce hatta zaɓen shekara ta 2015, lokacin da ƴan adawa a ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Buhari, ya kayar da shugaban Najeriya mai ci a wan chan lokaci Goodluck Jonathan, babban ci gaba ne ga ƙasar.
Kalli wannan bidiyo a sama don ganin cikakkiyar wannan hira.