Home Back

Jam'iyyar PRP Ta Bayyana Kuskuren Tinubu Wanda Ya Jefa 'Yan Najeriya Cikin Wuya

legit.ng 2024/6/28
  • Jam'iyyar adawa ta PRP ta caccaki manufofin tattalin arziƙin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsiro da su ƙasar nan
  • PRP ta ce ko kaɗan manufofin ba su dace ba domin babu abin da suka jawo sai wahala da shiga cikin halin ƙunci ga ƴan Najeriya
  • Ta yi kira ga gwamnatin da ta gaggauta sauya manufofin tare da mayar da hankali wajen yin abubuwan da su amfani ƴan ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PRP ta soki manufofin tattalin arziƙi da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke aiwatarwa a ƙasar nan.

Jam'iyyar PRP ta bayyana manufofin matsayin masu cutarwa ga al’ummar Najeriya.

PRP ta caccaki gwamnatin Tinubu
Jam'iyyar PRP ta soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu Hoto: @DOlusegun Asali: Facebook

PRP ta soki gwamnatin Tinubu

Jam'iyyar ta nuna takaicinta kan abin da ta bayyana yadda gwamnatin ba ta damu da halin ƙuncin da manufofinta suka jawowa ƴan Najeriya ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam'iyyar PRP na ƙasa, Dr. Falalu Bello, a cikin wata sanarwa ya ce wannan gwamnatin ba ta damu da wuyar da talaka ke sha ba, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.

Ya nuna cewa gwamnatin ta dogara kan wasu manufofin tattalin arziƙi na ƙasashen waje waɗanda tarihi ya nuna cewa ba su taɓa yin nasara ba.

PRP ta buga misalai da wasu manufofin da bankin duniya da hukumar IMF suka amince da su a shekarun baya, waɗanda suka jawo koma bayan tattalin arziƙi a ƙasashen Afirika da Latin Amurka.

Jam'iyyar wacce ta fi kowace daɗewa a ƙasar nan ta ce yawan ƙarin haraji da kuɗin ruwan da ake yi ya saɓawa hankali, musamman duba da yadda wuraren kasuwan ciki har da manya kamfanonin ƙasashen waje ke kullewa.

Ta kuma koka kan yadda masu kamfanoni ke shan wahala sakamakon cire tallafin man fetur, karya darajar Naira, ƙarin kuɗin lantarki da hauhawar farashin kayayyaki.

Wace mafita jam'iyyar ta kawo?

PRP ta yi nuni da cewa akwai hanyoyin tattalin arziƙi da za a bi waɗanda za su samar da abubuwan da ake buƙata ba kamar na yanzu ba da suka jawo wahala.

Ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta sauya waɗannan manufofin na ta, sannan ta buƙace ta da ta ba da fifiko wajen jin daɗin ƴan ƙasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading