Home Back

Jam'iyyar AfD mai ra'ayin kyamar baki na zarra a zaben EU

dw.com 2024/7/5
Wata mai kada kuri'a a zaben majalisar dokokin EU
Wata mai kada kuri'a a zaben majalisar dokokin EU

Kimanin Jamusawa milyan 360 ne zasu kada kuri'a, wanda kuma ke kasancewa zaben gama-gari na farko da al'ummar kasar zasu zabi mambobin majalisar dokoki baya ga zaben 2021 da kuma na 2025 da ke tafe.

Alkaluman farko da aka tattara ya nuna cewa jam'iyyar shugaban gwamnatin Jamus Scholz SPD ta samu kashi 15%, kasa da kashi  25.7% da jam'iyyar ta samu a zaben 'yan majalisar dokokin kasar a 2021.Lamarin dai bai yi wa kawancen jam'iyyun da ke tare da jam'iyyar SPD ta Mr. Scholz ba. A jamlace kawancen jam'iyyun da suka hada da jam'iyyar the Greens da liberal Free Democrats (FDP), sun sama kashi 35%.

A bangaren adawa kawancen jam'iyyun CDU da CSU sun yi samu gagarumar rinjaye da yawan kuri'u da ya kai kashi  30% a zaben EU, yayinda jam'iyyar AfD da ke kasancewa ta biyu a da'irar siyasar Jamus ta samu kashi 14%.

People are also reading