“NNPP Ta Barar da Damarta”: APC Ta Fadi Yadda Za Ta Kwace Mulkin Kano da Zamfara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jam'iyyar APC ta bugi kirji kan shirin kwace mulkin NNPP a jihar Kano da kuma PDP a Zamfara a zaben 2027.
Jam'iyyar ta ce duba da yadda jihohin suke bata lokaci kan wasu tsare-tsare da ke rage musu farin jin a jihohinsu, za su yi musu bazata.
Sakataren yada labaran jam'iyyar ta kasa a Arewa maso Yamma, Musa Mailafiya Mada shi ya bayyana haka yayin hira da jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mada ya ce a Kano mutane suna nadamar zaben NNPP saboda ta buge da wasu tsare-tsare da ba su taimakon talakawa.
Ya ce a Zamfara kuwa, Dauda Lawal yana aiki ne ga jam'iyyar APC saboda a kan tsaro ya gina yakin neman zabe kuma bai tsinana komai ba.
"NNPP kawai tana bata lokaci ne, sun buge da shirme da bai da amfani ga jama'a da suka hada da rusau da kuma rusa masarautun jihar."
"APC tana yiwa gwamnatin Kano godiya saboda tana ba ta kofar kwace mulki cikin sauki, jama'a da dama ba su son abin da ke faruwa a jihar."
"Yan Kano suna nadamar zaben NNPP tun yanzu, za mu yi amfani da hakan domin kwace mulki amma ba da shi kadai muka dogara ba."
- Musa Mada
Mada ya ce suna da dama sosai a Kano ganin shugaban APC da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa duk 'yan Kano ne.
A jihar Zamfara kuwa, Mada ya ce Gwamna Dauda Lawal sai bata lokacinsa ya ke yi wurin aibata gwamnatin da ta shude madadin aiki ga al'umma.
Kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta yi martani kan ci gaba da binciken Rabiu Kwankwaso da hukumar EFCC ke yi a Najeriya.
Jam;iyyar ta kalubalanci hukumar da ta kawo hujjoji kan binciken idan har ba bita da kullin siyasa ba ne kan sanatan
Asali: Legit.ng