Home Back

Ku taimakawa mabuƙata da Naman Sallah bisa halin matsin rayuwar da ake ciki – Limami

dalafmkano.com 2024/7/7

Babban limamin masallacin juma’a na Alaramma Abubakar Ɗan Tsakuwa, da ke unguwar Ja’en Ring road Mallam Abdulkareem Aliyu, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, da su kiyaye ƙa’idojin yanka Dabbobin Layyah, domin gujewa cin mushen Nama.

Mallam Abdulkareem Aliyu, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u, lokacin da yake tsokacin huɗubar da ya gabatar ranar Sallar Idin da ya jagoranta a masallacin ranar Lahadi 17 ga watan Yunin 2024.

Ya ce a mafi yawan lokuta al’umma sukan yanka dabbobi amma rashin bin ƙa’idojin yanka yakan sanya wa su ci mushen nama ba tare da sun sani ba, a dan haka su tashi tsaye wajen sanin yadda ake yanka Dabbobin a mahanga ta addinin Musulunci.

A cewar sa, “Musulmai ku kwaɗaitu da yin sadakar naman layya musamman ma ga masu ƙaramin ƙarfi domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T, “in ji shi”.

Mallam Abdulkareem Aliyu, ya kuma ce, akwai buƙatar a kiyaye nau’ikan dabbobin da aka sahale ayi layya da su, waɗanda suka haɗar da nau’in Sa ko Saniya, da kuma Raƙumi ko Raƙuma (Taguwar), ko kuma Rago ko Tinkiya, ko Akuya ko kuma Ɗan Akuya.

Wannan dai na zuwa ne bayan da al’ummar Musulmin Duniya suka gudanar da babbar Sallah, a jiya Lahadi 16 ga watan Yunin shekarar 2024.

People are also reading