Home Back

Minista Ya Ce Kirkirarriyar Basira ‘AI’ Za Ta Taimaka Wajen Kare Makarantu

leadership.ng 2024/7/1
Minista Ya Ce Kirkirarriyar Basira ‘AI’ Za Ta Taimaka Wajen Kare Makarantu

Karamin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Tanko Sununu, ya jaddada cewa amfani da kirkirarriyar basira (Artificial Intelligence) zai bunkasa da kyautata fasahohin da ake da su a bangaren koyarwa da tsaron makarantu.

Wanda ke magana a wajen taron kwararru kan fasahar sadarwar zamani na 2024 karo na goma sha takwas da ya gudana a Abuja.
A cewarsa, “Amfani da basirar AI a dukkanin makarantunmu zai taimaka mana wajen koyarwa, bibiya da kuma tabbatar da makarantunmu suna cikin tsaro.”

Ya ce, akwai gayar bukatar amfani da fasahohin zamani ciki kuwa har da na AI wajen karfafa wa sintiri da sanya ido kan muhallan makarantu, a cewarsa, “Ya zama dole a garemu mu rungumi yadda za mu tafiya da fasahohi, ciki har da na AI wajen aza tubalin bibiya da ayyukan sirri na tsawo da za su kaimu ga kare makarantunmu.”

Ya nemi taron kwararrun da cewa zai bullo da wasu hanyoyi da shawarorin yadda za su taimaka wa gwamnati wajen zuba na’urorin zamani kuma a tabbatar da sun yi aiki bisa hadin guiwa domin kyautata tattalin arziki, matakin fasaha, da wayar da kai kan tsaron kasar nan.

“Mun gani kuma muna kan ganin alfanu da fa’idar fasahar sadarwar zamani (IT) a karni na 21 da kuma irin rawar da take takawa wajen kyautata tattalin arzikin duniya.
“Mun kuma gano irin tasirin da take da shi wajen fadadawa da saukaka hanyoyin samun ilimi a dukkanin matakai,” ya shaida.

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta bi dukkanin matakan da suka dace wajen amfani da fasaha don ganin an samu nasarar bunkasa cigaba da rungumar fasahar sadarwar zamani a tsarin ilimin Nijeriya.

“Gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin ta kai Nijeriya da ajiyeta a matsayin shugaba a duniya, musamman a Afrika. Bangaren fasahar sadarwar zamani na taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan manufar da gwamnati ta sanya a gaba,” Sununu ya shaida.

Ya bukaci kwararrun da su mara wa yunkuri da shirin gwamnati baya gami da bada nasu gudunmawar domin cigaba da daurewar tattalin arzikin kasar nan.

People are also reading