Home Back

Kenya: 'Yan sanda sun kashe gomman mutane a 2023

dw.com 2024/5/5

Kungiyoyin da suka hada da Human Rights Watch da Amnesty International da kuma Kenya group Missing voices sun ce rabin kashe-kashe an aikata ne a lokacin da ake gudanar da ayyukan yaki da miyagun laifuka.

Yayin da mutane 45 an kashe su ne a lokacin da aka yi zanga-zangar 'adawa da tsadar rayuwa a kasar da aka gudanar a tsakanin watannin Maris da kuma Juli na shekarar bara.

Rahoton kungiyoyin ya kuma ce, ba kasafai ake kama 'yan sandan suka aikata kisan gilla da kuma hannu wajen batar mutane. Sai dai kuma Kakakin rundunar 'yan sandan Kenya, Resila Onyango bata mayar da martani kan lamarin ba.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun sha zargin jami'an 'yan sandan Kenya da amfani da karfin tuwo kan jama'a mussaman a unguwannin 'yan rabbana ka wadata mu, sai dai kuma gwamnatin kasar ta dade ta na cewa tana daukar mataki.

People are also reading