Home Back

Ondo: Jam'iyyar APC Za Ta Bayar da Satifiket Din Lashe Zaben Fidda Gwani

legit.ng 2024/5/17
  • Jam'iyyar APC mai mulki za ta gabatar da satifiket ɗin lashe zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar Ondo, ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa
  • Mataimakin sakataren tsare-tsaren jam'iyyar na ƙasa ne ya tabbatar da cewa za a ba gwamnan satifiket ɗin ne a ranar Litinin, 29 ga watan Afirilun 2024
  • Gwamnan shi ne dai ya zama ɗan takarar gwamnan jam'iyyar a zaɓen da za a gudanar a watan Nuwamban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Jam’iyyar APC za ta miƙawa wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar Ondo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa, satifiket ɗin lashe zaɓe a ranar Litinin.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi nasarar lashe zaɓen ne wanda aka gudanar domin fidda ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamba.

APC za ta gwamnan Ondo satifiket
Gwamna Lucky Aiyedatiwa zai karbi satifiket din lashe zaben fidda gwanin gwamnan Ondo Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa Asali: Facebook

Mataimakin sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na ƙasa, Nze Duru ne ya bayyana hakan ga jaridar The Punch a ranar Lahadi, 28 ga watan Afirilun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a bada satifiket ɗin?

"Eh ranar Litinin ne za a gabatar da takardar shaidar cin zaɓen ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke Abuja."

- Nze Duru

Sai dai Duru bai bayyana ko za a gabatar da satifiket ɗin ne a gabanin taron kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ko a lokacin taron ko bayan an kammala, wanda shi ma za a yi a ranar Litinin.

Hakan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga ƴan takarar da suka fafata a zaɓen da su marawa Gwamna Lucky Aiyedatiwa baya.

Kwamitin zaɓen fidda gwanin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Usman Ododo ne ya ayyana Ayiedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan kammala gudanar da zaɓen a dukkanin ƙananan hukumomin jihar 18.

Sai dai, wasu daga cikin ƴan takarar sun ƙalubalanci sakamakon zaɓen bisa zargin tafka maguɗi da tashe-tashen hankula a wasu rumfunan zaɓe.

APC za ta yi rashin nasara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Ondo, ya hango rashin nasara ga jam'iyyar a zaɓen gwamnan jihar.

Bamidele Oloyeloogun ya yi nuni da da cewa APC ka iya yin rashin nasarar ne idan ba a soke zaɓen fidda gwani na gwamna da ta yi ba a jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading