Home Back

Babu Tabbacin Dawo da Kudin Tallafin Wutar Lantarki Inji NERC

legit.ng 2024/5/2
  • Shugaban hukumar kula da wutar lantarki na kasa, Garba Musa, ya ce babu tabbas a kan za a yi nasarar dawo da tallafin lantarki saboda kiran da 'yan Najeriya suke yi
  • Shugaban ya kara da cewa har yanzu ana bin gwamanti bashin biliyoyin kudade akan tallafin wuta na shekarar 2023
  • Ya yi bayanin ne jiya Alhamis yayin tattaunawa da shugabannin majalisar wakilai a kan kira da suka yi a dawo da tallafin wuta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Hukumar kula da samar da wutar lantarki ta kasa (NERC) ta ce babu tabbas akan dawo da tallafin lantarki a Najeriya.

Hukumar ta ce idan za a dawo da tallafin a halin yanzu to dole sai gwamnati ta kashe sama da naira triliyon 3 a shekarar 2024 kawai.

NERC Nigeria
Hukumar samar da wutar lantarki ta kasa ta ce lantarki ba za ta samu a Najeriya ba matukar aka zuba wa gwamnati ido kan tallafi. Hoto: Transmission Company of Nigeria Asali: Facebook

Shugaban hukumar ne, Sanusi Garba, ya fitar da bayanin a jiya Alhamis yayin tattaunawa da 'yan majalisar wakilai ta kasa masu kula da kwamitin wutar lantarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya tabbatar wa 'yan majalisar cewa kudin da gwamnati ke sakawa a harkar wutar lantaki ba zai iya samar da wuta a kasar ba.

Sobada haka idan aka cigaba da zuba wa gwamnati ido a harkar wuta, lantarki za ta durkushe a kasar baki daya, cewar jaridar Leadership.

Sharadin dawo da tallafin lantarki

Shugaban ya kuma ce idan har ana so a dawo da tallafin to dole gwamnati ta shirya biyan sama da triliyon 3 domin biyan tallafin shekarar 2024.

A yayin da yake bayyana cewa babu tabbas akan cewa gwamnatin za ta iya biyan kudin, ya nuna cewa har yanzu gwamantin ba ta gama biyan kudin tallafin shekarar 2023 ba.

Ya ce har yanzu ana bin gwamanti bashin sama da naira biliyan 400 na shekar 2023 kuma har yanzu ba a san ranar da za ta biya ba, kamar yadda jaridar the Punch ta nakalto.

Martanin majalisar wakilai

Ana shi martanin, wakilin majalisar a kan harkokin samar da wutar lantarki, Victor Nwakolo, ya ce har yanzu suna kira ga gwamnatin ta kara duba lamarin.

A cewarsa duba lamarin kusan ya zaman wajibi ne, musanman duba layin 'yan Banda A da sauransu.

Majalisa ta yi magana kan tallafin wuta

A wani rahoton kuma, kun ji cewa yayin da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi kokarin cire tallafin wutar lantarki a Najeriya, Majalisar Dattawa ta ce ba ta amince ba lura da halin kunci da al'ummar kasar ke ciki.

A lokacin majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta janye aniyarta na janye tallafin wutar lantarki har sai al'amura sun fara sauki a kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading