Home Back

Yadda Aka Kashe Mutum Shida Da Sace Wasu Ranar Sallah A Sokoto

leadership.ng 2024/11/4
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi

Akalla mutane shida ne rahotanni suka ce an kashe tare da yin garkuwa da mutane sama da 100 yayin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wa wata al’umma hari a Jihar Sokoto.

Rundunar ‘yansanda sa Jihar Sokoto, ta bakin mai magana da yawunta, Ahmed Rufa’i, ta tabbatar da kashe mutum sama da 6 tare da yin garkuwa da dama a Tudun Doki da ke Karamar hukumar Gwadabawa a Sokoto.

Rufa’i ya ce duk da cewa har yanzu ana tattara bayanai game da harin, amma an tabbatar da mutuwar mutum shida.

A cewarsa, jami’in ‘yansandan shiyya da ke Gwadabawa ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa al’umma domin duba lamarin tare da dawo da zaman lafiya.

Akalla mutum shida ne rahotanni suka ce an kashe tare da yin garkuwa da mutane sama da 100 yayin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wa wata al’umma hari a Jihar Sokoto.

“Rundunar bincike ta gano gawarwaki shida kuma ana ci gaba da kokarin kwato sauran mutanen da suka bata,” in ji kakakin ‘yansandan.

A cewar mazauna kauyen, maharan wadanda adadinsu ya kai kusan bakwai, sun far wa al’ummar da misalin karfe 1:30 na safe dauke da manyan bindigogi, sun harbin kan mai uwa da wabi inda suka yi awon gaba da ’yan uwa da dama.

Gwadabawa, daya daga cikin kananan hukumomin da ke Gundumar Sanata ta Gabas ta Jihar Sakkwato, ta kasance cikin kwanciyar hankali har zuwa harin da aka kai.

A halin da ake ciki dai sojojin Operation Whirl Punch sun ci gaba da kai samame tare da sintiri a Jihar Kaduna inda suka kashe wasu ‘yan bindiga uku a hanyar Gonna Rogo-Eka a Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Gida Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Majiyarmu ta ruwaito cewa, a ranar 14 ga watan Yuni, sojojin sun kashe ‘yan bindiga 36, ciki har da Buhari Alhaji Halidu, wanda aka fi sani da “Buharin Yadi,” daya daga cikin manyan ‘yan fashin da suka addabi Arewa.

Bayan kashe-kashen, mazauna yankunan kan iyakar Kaduna da Katsina sun shiga cikin farin ciki.

A wani samame na baya-bayan nan, kwamishinan ya ce, “Dakarun da ke aikin sintiri sun kashe ‘yan bindiga uku a yankin Gonna Rogo-Eka na Karamar Hukumar Kajuru.”

Ya kara da cewa an kwato bindigogin AK-47 guda biyu, kwanson AK-47 guda hudu da harsashi 81 na 7.62mm bayan wani kazamin fada aka gwabza da ‘yan fashin.

“Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce sojojin sun gudanar da sintiri na musamman a yankin inda suka samu ‘yan bindigar. Bayan musayar wuta, an kashe uku daga cikin masu laifin a takaice.

Gwamna Uba Sani, da yake magana a kan ci gaban, ya gode wa jami’an tsaro tare da yaba wa dakarun da ke karkashin jagorancin babban kwamandan runduna ta daya ta sojojin Nijeriya, Manjo Janar M.L.D Saraso, kan yadda suka kara kaimi wajen ganin an gudanar da bukukuwan Sallah lami lafiya. ‘yan kasa.