Home Back

An Sace ’Yan Makaranta 1680, an Kashe Sama da 180 a Shekaru 10 a Najeriya Inji UNICEF

legit.ng 2024/5/18
  • Binciken Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da cewa a tsawon shekaru 10 an sace 'yan makaranta sama da 1680 a Najeriya
  • Kwararriya a fannin sadarwa ta UNICEF, Susan Akila, ce ta fitar da bahasin yayin wani biki domin tinawa da 'yan matan Chibok bayan shekaru 10 da sace su
  • Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga gwamnatin Najeriya domin inganta tsaro a makarantun kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tarayyar Nigeria - Sama da 'yan makaranta 1,680 ne aka sace tare da kashe kusan 180 a hare-haren da 'yan ta'adda suka kai a makarantun Najeriya cikin shekaru 10 da suka gabata.

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ne ya fitar da bahasin yayin cika shekara goma da sace 'yan matan Chibok a wani rahoto.

Tinubu
Hare-hare kan makarantu na cigaba da barazana ga karatun yara a Najeriya. Hoto: Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Kwararriya a fannin sadarwa ta UNICEF, Susan Akila, a cikin wata sanarwa da ta fitar domin tunawa da shekaru 10 da aka sace ‘yan mata a makarantar Chibok, ta bukaci a dauki matakin bada kariya ga ilimin yara a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta koka da cewa shekaru 10 bayan sace yara ‘yan makaranta na farko a Najeriya, ana ci gaba da kai hare-hare a akalla makarantu 70 a cikin jihohi 10 masu fama da matsalar tsaro, cewar jaridar Vanguard

Hakan ya nuna cewa an dauki tsawon shekaru ana sace dalibai da malamai da dama a fadin Najeriya.

A cewar rahoton CNN, a watan Maris din shekarar 2024, sama da dalibai 300 ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka sace a makarantar firamare da ke kauyen Kuriga, a gundumar Chikun ta Kaduna.

A watan Maris din 2018, 'yan Boko Haram sun sace 'yan matan makaranta fiye da 100 a garin Dapchi da ke jihar Yobe, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Hakan nan dai Premium Times ta kuma ruwaito cewa ‘yan bindiga sun sace dalibai 10, da malami a Katsina a watan Agusta, 2021.

Adadin daliban da aka sace a Najeriya

Hare-haren sun kai ga yin garkuwa da ɗalibai wanda a cikin shekaru 10 da suka gabata, tashe-tashen hankula masu nasaba da rikici sun kai ga sace daruruwan yara.

Sama da yara 1,680 aka sace a lokacin da suke makaranta da sauran wurare; Yara 180 ne suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai a makarantu.

An yi garkuwa da ma’aikatan makarantar 60 an kuma kashe 14, da kuma hare-hare sama da 70 a makarantu.

Barazanar sace dalibai na yin illa ga karatun yara sosai. Ya zuwa shekarar 2021, sama da yara miliyan daya ne ke tsoron komawa makaranta.

Rahoton UNICEF ya ce a shekarar 2020, an rufe makarantu kusan 11,500 saboda hare-hare, in ji UNICEF.

Kira ga gwamnatin Najeriya

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi kira da a kara kaimi wajen kare al’ummar kasar da suka fi fama da ‘rashin tsaro.

Wani sabon rahoton UNICEF ya nuna cewa kashi 37 cikin 100 na makarantu a jihohi 10 ne kawai ke da tsarin kariya ga hare-haren makarantu.

Hanyoyin kare makarantu

UNICEF a Najeriya ta bukaci gwamnati, masu ruwa da tsaki da kasashen duniya da su dauki kwakkwaran mataki domin kare makarantu

Matakan sun kun shi tabbatar cewa duk makarantu a faɗin jihohi suna da kayan aikin da za su aiwatar da mafi ƙarancin ƙa'idodin makarantu masu aminci.

Ciki harda karfafa jami'an tsaro da matakan tsaro don kare cibiyoyin ilimi da al'umma daga hare-hare da sace-sace.

Asali: Legit.ng

People are also reading