Home Back

Matasa Sun Yi Ajalin Yunusa Kan Zargin Furta Kalaman Batanci ga Fiyayyen Halitta a Bauchi

legit.ng 2024/6/29
  • An shiga wani irin yanayi a jihar Bauchi bayan wasu matasa sun yi ajalin matashi kan zargin kalaman ɓatanci
  • Ana zargin Yunusa wanda ɗan Faira ne da furta kalamai marasa daɗi ga Annabi Muhammad (SAW) a jihar
  • Lamarin ya faru ne a kauyen Nasaru da ke karamar hukumar Bauchi a jiya Laraba 19 ga watan Yunin 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Wasu matasa sun yi ajalin wani a jihar Bauchi kan zargin batanci ga fiyayyen halitta.

Matasan sun yi ajalin matashin ne mai suna Yunusa a kauyen Nasaru da ke karamar hukumar Ningi a jihar.

Lamarin ya faru ne a jiya Laraba 19 ga watan Yunin 2024 kan zargin kalamai marasa daɗi ga Annabi Muhammad (SAW), cewar Tribune.

Yunusa kamar yadda shaidun gani da ido suka fada ya furta kalaman ne yayin da suke musu mai zafi.

"Yunusa ya kasance ɗan Faira ne, ya furta wasu malamai da ba su dace ba, inda aka bukaci ya janye ya ki, har aka fara dukansa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bayan bukatar ya janye kalaman nasa sai ya ki tare da maimaita su daga nan ne mutane suka farmasa."

- Cewar majiyar

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan sanda sun yi kokarin cetonsa amma mutane sun fi karfinsu inda suka yi amfani da sanduna da duwatsu wurin hallaka shi.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading