Home Back

Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (4)

leadership.ng 2024/6/30

Ci gaba daga makon jiya

Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (4)

A shafi na arba’in da hudu, sakin layin farko, an rubuta makaniken, maimakon bakaniken. A karshen sakin layin aka rubuta suka sharara a guje, maimakon suka sheka a guje.

Sai sakin layi na kusa da na karshe da aka rubuta eh? Maimakon iyeh? A dai shafin an rubuta ka ke, maimakon kake.

Haka nan a shafi na arba’in da takwas sakin layi na farko an rubuta ya kan, maimakon yaka. A sakin layi na uku a shafin na arba’in da biyar an rubuta Babbar Salla, maimakon Babbar Sallah. A sakin layi na hudu aka rubuta ta, maimakon Ta. An rubuta ka ke, maimakon kake. Sai sakin layi na kusa da na karshe da aka rubuta kome, maimakon komai.

Sai a shafi na arba’in da bakwai babi na shida sakin layi na farko da aka rubuta gwarhii, maimakon gwarhi. A sakin layi na uku a shafin an rubuta kakume, maimakon kwakume. Sai sakin layi na gaba da aka rubuta kukan jirgi, maimakon karar jirgi, ko kugin jirgi.

A shafi na arba’in da takwas sakin layi na biyar an rubuta Sidi ya gandara karya, maimakon Sidi ya kantara karya. A shafi na hamsin an rubuta hukeken, maimakon mukeken. A shafi na hamsin da daya sakin layi na karshe an rubuta ba tare tikiti ba, maimakon ba tare da tikiti ba. A shafi na hamsin da uku an rubuta Sunana, maimakon Suna na. A kalmar karshe a shafin na hamsin da uku an rubuta brekfast. In ana so a Hausantar da kalmar sai a rubuta burekfas. In kuma za a bar ta a yadda take a Ingilishi ne, sai a rubuta breakfast. Amma ba brekfast ba. Fassara ita ce tara. Misali ‘yan makaranta sun fito tara. Sai dai na lura a yanzun da karfe goma ake fitowa tara don karin kumallo.

A shafi na hamsin da hudu an rubuta dogon, maimakon Dogon. An rubuta shine, maimakon a rubuta shi ne. An rubuta Mai’unguwan Dusi, maimakon Mai Unguwar Dusi.

A babi na bakwai, shafi na hamsin da bakwai, sakin layin farko an rubuta nim, daga kalmar Ingilishi ta neem wato dalbejiya ko dogon yaro. Tunda kwai sunan a Hausa da bai kamata a aro kalmar Ingilishi ba. Haka ma a shafi na tamanin da biyu.

A shafin na hamsin da bakwai sakin layi na biyu inda aka rubuta ‘bayansa kuma masu kakaki, fare, kaho da algaita…’ Maimakon ‘bayansa kuma masu kakaki, da fare, da kaho da algaita…’

A shafi na 58 sakin layi na kusan uku an rubuta “Haba Sidi, nh?” Kalmar karshe ce ta nh ban san da ita a Hausa ba. Haka nan a sakin layi na farko shafi na tamanin da biyar. Haka nan a layi na biyu a sakin layin an sa ya ke, maimakon yake.

Sai shafi na hamsin da tara sakin layi na karshe an rubuta ‘A Raki Sidi ya sami babban aboki a Yahaya. Ban san me wasalin a ke yi a cikin jimlar ba.

A shafi na 60 sakin layi na biyu inda aka rubuta “Badi in Allah ya so zai dauki jarabawar zuwa babbar makaranta” Maimakon “Badi in Allah Ya so zai rubuta jarabawar zuwa babbar makaranta” Har ila yau a shafin na 60 sakin layi na uku jimla ta biyu an rubuta ‘Sidi, Yahaya da Olu…’ Maimakon ‘Da Sidi da Yahaya da Olu…’ Haka ma a sakin layi na karshe, da sakin layi na farko shafi na sittin da bakwai. Haka ma a shafi na 77.

Sai sakin layi na hudu da aka rubuta gwaba maimakon gwaiba. Sai shafi na sittin da daya inda aka rubuta takule shi maimakon takale shi.

Sai magana ta kusa da sakin layi na karshe da ba a fayyace maganar wane ne tsakanin Sidi da Olu da ke kasan mangwaro.

A sakin layi na karshe an rubuta fintinkyau maimakon fintinkau. Sai shafi na sittin da uku sakin layi na farko da aka rubuta Yahaya bi sauko ba, maimakon Yahaya bai sauko ba. A karshen sakin layi na biyu an rubuta 4:30 p.m. Maimakon hudu da rabi na yamma ko 4 da rabi na yamma.

A shafi na sittin da bakwai an manta ba a sa alamar tambaya a karshen jimlar farko sakin layi na uku ba. A shafi na saba’in da hudu an rubuta Hakanan, maimakon Haka nan. Haka ma a shafi na tamanin da daya sakin layi na karshe.

A shafi na saba’in da daya babi na tara kanun babin an rubuta SIDI YA KARYE KAFA, Maimakon SIDI YA KARYA KAFA. Haka nan a maganar farko a babin an rubuta

“Me ka ke yi haka,” ya tambayi Sidi. Maimakon

“Me kake yi haka?” Ya tambayi Sidi.

A dai shafin an rubuta Albirinku maimakon Albishirinku. Sai kuma shafi na tamanin da hudu sakin layi na uku da aka rubuta Salla maimakon Sallah. Sai jimla ta gaba da aka rubuta Yahaya, Jauro, Hassana da Olu… Maimakon Yahaya, da Jauro, da Hassana da Olu…

Haka nan a sakin layi na gaba an rubuta Sekondare, maimakon Sakandare.

Sai shafi na karshe jimlar farko da aka rubuta in ji, maimakon In ji. Sai gaba da aka rubuta Allah ya yarda, maimakon Allah Ya yarda.

Kalmomin Aro daga Ingilishi

Sai kalmomin da aka aro daga Ingilishi da suka fito a cikin littafin.

Dina daga Dinner

Filasta daga Plaster

Sekondare daga Secondary

Nim daga Neem

Gwaba daga Guaba

Brekfast daga Breakfast

Tasin daga Tadi

Tikiti daga Ticket

Koleji daga College

Afril daga April

Landiroba daga Land Rober

Makanike daga Mechanic

Kammalawa

Sidi ya Shiga Makaranta na Umaru Ladan da Michael Crowder, ainihinsa littafi ne na Ingilishi Sani Goes to School aka fassara zuwa Hausa don saukin fahimta, har kuma ya yi nasarar shiga sahun littafan da aka zabo don manhajar makarantu. Sai dai da yake duk dan adam ajizi ne wato tara muke ba mu cika goma ba, an samu wasu ‘yan kurakurai da idan aka dube su da idon basira aka gyara, ko shakka babu littafin zai tsere wa tsara.

People are also reading