Home Back

Zamu baza jami’an mu 3,168, domin samar da tsaro a bikin babbar Sallah a Kano – Civil Defense

dalafmkano.com 2024/7/6

Rundunar tsaro ta Civil Defence da ke nan Kano, ta ce za ta baza jami’anta akalla su dubu 3,168, da za suyi haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro a jihar nan, domin samar da tsaro a yayin, da lokacin, da kuma bayan bikin babbar Sallah, da ke kara gabatowa.

Kwamandan rundunar Civil Defence din jihar nan Kano Muhammed Lawal Falala, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a yammacin yau Juma’a 14 ga watan Yunin 2024.

Sanarwar ta kuma ce, rundunar za tayi hadin gwiwa da jami’an tsaron ‘yan sanda, da na farin kaya DSS, da kuma na Karota, da na hukumar kiyaye afkuwar haɗura Road Safety, da sauransu, domin tabbatar da tsaro a fadin jihar Kano.

Da yake yiwa gidan rediyon Dala FM Kano, karin bayani mai magana da yawun rundunar tsaron SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya ce rundunar su na bukatar hadin kan al’umma domin ganin an gudanar da bukukuwan sallar cikin lumana da kwanciyar hankali.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da bikin
babbar Sallah, wanda za’ayi tsayuwar Arafa a gobe Asabar 15 ga watan Yunin 2024.

People are also reading