Home Back

Saudiyya na farauta Casemiro, Greenwood na son komawa Sifaniya

bbc.com 2024/7/5
Casamero

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyoyi da dama a Saudiyya da suka hada da Al Nassr da Al Ahli da Al Qasidiya na farautar ɗan wasan Brazil daga Manchester United, Casemiro mai shekara 32 da ke buga tsakiya. (Goal - in Portuguese)

West Ham ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 15 kan ɗan wasan Flamengo mai shekara 28 daga Brazil, Fabricio Bruno. (Guardian)

Ɗan wasan gaba a Manchester United da Ingila, Mason Greenwood na son ya koma ƙungiya Getafe na Sifaniya a kaka mai zuwa bayan matashin mai shekara 22 ya buga wasansa na karshe a matsayin ɗan aro a ƙungiyar. (TEAMtalk)

Aston Villa da Crystal Palace na farautar ɗan wasan Ingila mai shekara 22 da ke tala leda a Gent, Archie Brown. (Mirror)

Barcelona na kokarin ganin ta sayo ɗan wasan gaba a Portugal Joao Felix daga Atletico Madrid a karo na biyu bayan matashin mai shekara 24 ya kammala zaman aronsa a Nou Camp. (Sport - in Spanish)

Newcastle na kokarin ganin ta cimma burinta na saye ɗan wasan Ingila Tosin Adarabioyo, mai shekara 26 da ke shirin barin Fulham a wannan kaka da zaran kwantiraginsa ya kare. (Talksport)

Liverpool ta sanya fam miliyan 20 kan ɗan wasan Dutch mai shekara 22, Sepp van den Berg, da ƙungiyoyi irinsu Brentford, Southampton da Wolfsburg ka farauta bayan kammala zaman aro a Mainz. (Athletic, subscription required)

Napoli ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan Georgia, Khvicha Kvaratskhelia mai shekara 23 ga Paris St-Germain, yayinda Antonio Conte ke gab da karban aikin kociyanta. (Corriere dello Sport in Italian), external

Ɗan wasan Brazil a Real Madrid Rodrygo mai shekara 23, na cikin rashin tabbas kan makomarsa, yayin da ake tunanin zai je Liverpool. (Mundo Deportivo - in Spanish, via Dazn)

Tottenham za ta duba yiwuwar sayar da ɗan wasanta na Ingila mai shekara 23, Djed Spence da kuma na Sifaniya da ke buga gefe Bryan Gil, mai shekara 23, a wannan kaka. (Football Insider)

Ana jayayya kan dan wasan RB Leipzig na Sifaniya, Dani Olmo, inda Barcelona da Manchester United da Manchester City da Liverpool da Bayern Munich kowanne ke nuna zawarcinsa kan matashin mai shekara 26. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Southampton na bibbiyar ɗan wasan Sunderland mai shekara 23, Jack Clarke. (Telegraph - subscription required)

Inter Milan na farautar ɗan wasan Ingila mai shekara 26, Aaron Wan-Bissaka, wanda Manchester United ta yiwa kudi yuro miliyan 12. (£10.2m). (Tuttomercatoweb - in Italian)

Arsenal da kociyanta Mikel Arteta na tattaunawa kan sabunta kwantiraginsa mai tsaye a ƙungiyar. (Football Insider), external

Xavi na son sayar da ɗan wasansa mai shekara 35 daga Poland, Robert Lewandowski a wannan kaka. (Sport - in Spanish)

People are also reading