Home Back

‘Yar Sanda Da Wata Sun Shiga Hannu Kan Sato Yara 5 Daga Sakkwato

leadership.ng 2024/5/18
Uba Ya Hallaka Dansa Daya Tilo Kan Cacar-baki

Wata ’yar sanda mai mukamin ASP da wata mai taimaka mata sun shiga hannu bisa zargin sato kananan yara biyar daga Jihar Sakkwato zuwa Abuja.

Ana zargin ’yar sandar, ASP Kulu da sato yaran ciki har da jaririya ’yar makonni biyu da haihuwa.

’Yansandan sun kama ASP Kulu da mai taimaka mata a Abuja, lokacin da suke dawowa daga Sakkwato a cikin bas din haya mai dauke da mutane 18.

Ana tsakar tafiya ne dai sauran fasinjojin suka lura cewa babu wadda ta shayar da jaririyar ‘yar makonni biyu.

Wani fasinja a motar ya ce: “A ranar Asabar 27 ga watan Afrilu muna cikin tafiya sai muka lura yaran ba sa cikin hayyacinsu kuma ba sa magana.

“Don haka, yayin da muka sauka a Deidei, sai muka tambaye su don tabbatar da ko ’ya’yansu ne, sai suka ce eh, ’ya’yansu ne.

“Ita ’yar sandar da ke rike da jaririyar ta shaida mana cewa ba ta iya shayar da ita ne saboda tana fama da ciwon nono.

“Muna jin haka sai muka sanar da ’yansanda kuma da zuwa suka kai wadanda ake zargin ofishinsu da ke Gwagwa.

“A jiya Litinin kuma aka tura su zuwa babban ofishin ’yansanda na Abuja tare da yaran da suka sato.”

An gano ASP Kulu, tana aiki da rundunar ’yansanda a yankin Kubwa da ke Abuja.

An kuma gano cewa akwai wasu yaran da ke gidanta a Deidei, kuma shaidu sun tabbatar da ganin ta da yara da dama a makonnin da suka gabata.

Kakakin rundunar Abuja, SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce suna gudanar da bincike.

People are also reading