Home Back

Aikin Kwankwaso ne: Lauyan APC ya 'Tona' Masu Neman Karya Ganduje a Siyasa

legit.ng 2024/5/19
  • Jam'iyyar APC ta yi zargin tsohon Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso na kokarin kawo nakasu a siyasar shugabansu, Abdullahi Umar Ganduje gabanin 2027
  • Lauyan jam'iyyar, Farfesa AbdulKareem Kana ne ya yi zargin, inda ya ce shugabannin biyu sun dade tare, kuma akwai yiwuwar su sasanta junansu a siyasance
  • Sai dai NNPP ta yi martani da cewa APC rikitacciyar jam'iyya ce, kuma ba komai da shugabanta, Ganduje ya fada za su mayarwa martani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Jam’iyyar APC ta sake zargin jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kokarin dunkufe tauraruwar shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje gabanin kakar zabe mai zuwa.

Mai ba jam’iyyar shawara ta fuskar shari’a, Farfesa AbdulKareem Kana ne ya bayyana haka a shirin siyasa ta tashar Channels Television.

Abdullahi Umar Ganduje
Lauyan APC, AbdulKareem Kana ya zargi Kwankwaso da kokarin dakile siyasar Ganduje gabanin zaben 2027 Hoto: @OfficialAPCNg, Rabiu Musa Kwankwaso Asali: Twitter

Kwankwaso yana da hannu a rikicin APC?

Farfesa Kana ya kara da cewa kwararan hujjoji sun nuna cewa shugabancin NNPP da sauran jagororinsu a Kano ne ke daukar nauyin zanga-zangar neman cire Ganduje daga shugabancin APC, kamar yadda Punch News ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce duk da bai san dalilan barakar da ta shiga tsakanin Kwankwaso da Ganduje ba, amma sanin kowa ne cewa dukkaninsu biyun gogaggun ‘yan siyasa ne, kuma ya na da yakinin za su iya sasanta junansu.

“APC ta shiga rudani,” NNPP

A martaninsa, sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP na kasa, Ladipo Johnson ya bayyana APC da rikitacciya jam’iyya kuma mai rudadden shugaba.

“Ba mu son mayar da martani kan duk wani abu da GanTduje ko APC suka fada. Babu ruwan kwankwaso cikin matsalar da Ganduje ke fuskanta, matsala ce da ya janyo da kansa,” inji sakataren.

“Da wahala Ganduje ya rasa kujerarsa,” Lauya

Mun ruwaito muku cewa lauyan jam’iyyar APC, AbdulKareem Kana ya ce zai yi wahala matuka Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya rasa kujerarsa na shugabancin jam’iyyar.

Farfesa AbdulKareem Kana ya kara da cewa ba a bi hanyar da doka ta shimfida wajen dakatar da shugaban daga jam’iyyar ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading