Home Back

Me ke faruwa da Adam A. Zango?

bbc.com 2024/5/3

Asalin hoton, Adam A Zango

Adam Zango
Bayanan hoto, Zarge-zargen da Adam A. Zango ya yi wa matansa da abokan sana'arsa ne suka fi jan hankalin ma'abota shafukan zumunta

A shekaru kamar 15 da suka wuce, duk wanda ya san tauraron Kannywood Adam A. Zango ya san shi ne da jan hankalin masoyansa a finafinai, yanzu kuma hakan ya fi yawa a shafukan sada zumunta.

Ma'abota shafukan zumunta, masu bin Adam Zango da waɗanda ma ba su bin sa, sun wayi garin Lahadi da labarai iri-iri daga shafin babban tauraron cikin bidiyon da wallafa amma kuma ya goge daga baya.

Mafi girma daga cikinsu shi ne inda yake batun dalilan da suka sa ya rabu da mata shida da ya aura a baya, da kuma sunan wasu abokan sana'arsa na Kannywood.

Sai dai mutane da dama ba za su yi mamakin maganganun na Zango ba saboda da ma an san shi da bayyana abubuwan da suke damun sa a lokuta daban-daban.

Amma abin da ya sa wannan karon lamarin ya bambanta da saura shi ne, da ma ya sanar da mabiyansa cewa zai bayyana dalilan a fili don masu zargin sa su yi hukunci, kamar yadda bayyana a Instagram kafin ya goge.

Sai dai tambayar da mutane da dama suka kasa samun amsarta ita ce: me ke damun Adam Zango?

'Ni kaɗai na san larurar damuwar da na shiga'

Asalin hoton, Facebook/Adam Zango

Adamu Zango
Bayanan hoto, Adam A. Zango ya shafe shekara sama da 20 a Kannywood

Masoya da masu amfani da shafukan zumunta sun daɗe da sanin cewa Adam Zango ba shi ɓoye batun tsananin damuwa - wato depression a Turance - da ya sha shiga a baya, kuma yana yawan bayyana damuwarsa kan abubuwan da suka shafe shi a filin Allah.

Kazalika, tauraron ya sha alaƙanta hakan da irin wahalar da ya sha a kan hanyarsa ta zama abin da ya zama a masana'antar fim zuwa yanzu, inda ya zama jarumi, mawaƙi, kuma mai shirya fina-finai.

"Ina ɗaya daga cikin mutanen da suka fi kowa haɗuwa da ƙalubale a wannan masana'antar tamu, na daku ne," kamar yadda Zango ya faɗa wa Madina Maishanu yayin wata hira da BBC Hausa ta cikin shirin Mahangar Zamani.

Cikin hirar da aka yi a watan Fabarairun 2024, an tambayi Zango ne kan kwana biyu ba a jin ɗuriyarsa sosai a Instagram, inda Madina ta sake tambayarsa cewa "me ya faru ne, ka ba mu labari mana.

Sai ya ba da amsa da cewa: "Babu wanda yake yin magana ta zama wani babban abu a masana'antar kamar ni. Idan mutum 100 suka yi magana babu mai kula su, amma idan na yi ɗaya sai an yi mata reshe kamar 100."

Kafin haka, an ga Adam Zango na bayyana cewa ya shiga tsananin damuwa a lokuta daban-daban cikin wani bidiyo da ya ɗauka da hannunsa.

"Ni kaɗai na san adadin yawan tsananin damuwar da na shiga a rayuwa kuma hakan ta faru ne saboda shuru [da nake yi]," in ji shi cikin bidiyon da ya wallafa a shafin zumuntarsa - wanda ya goge shi a yanzu.

A gefe guda kuma, Zango ya musanta cewa larurar damuwa ce ta sa ya wallafa kalaman na baya-bayan nan.

"Lafiyata ƙalau babu abin da ya same ni. Na ga wasu na cewa kamar na zare ne, ina so na kashe kaina ɗin nan...ba ni da depression tura ce kawai ta kai bango," kamar yadda aka gan shi cikin wani bidiyo yana faɗa a safiyar Litinin.

Shi ma Ali Nuhu - shugaban hukumar finafinai ta Najeriya kuma babban tauraro a Kannywood - ya ce bincikensu ya nuna cewa lafiyarsa ƙalau.

"Lafiyarsa ƙalau. Wani lokacin wasu kan ɓata mana rai saboda 'yan'adam ne mu. Mun gode da kula da kuma damuwar da kuka nuna," a cewarsa cikin wani saƙo a Instagram.

Ƙwarin gwiwar da Adam Zango ke da shi wajen mayar wa mutane martani a fili na da girma sosai, musamman idan aka yi la'akari da rikice-rikicen da ya yi da wasu a baya.

Idan ba a manta ba, rikicin da ya faru tsakaninsa da Ali Nuhu ya yi ƙamarin da sai da Zango ya yi barazanar kai ƙara kotu bisa zargin an zagi mahaifiyarsa.

A lokuta daban-daban kuma ya sha jaddada aniyarsa cewa duk wanda ya taɓa shi "indai ya haɗa da addini to wallahi sai na yi magana".

Ya ce: "In ka ga ban yi magana ba to a kan hassada ce da ƙyashi wani ya yi magana a kaina. Idan wannan ne ba zan ba shi amsa ba saboda an wuce wannan lokacin."

'Abubuwan da suka jefa ni cikin damuwa'

Adam Zango
Bayanan hoto, Adam Zango ya faɗa wa BBC cewa ya sauka daga batun ba zai sake yin aure ba

Duk lokacin da Adam Zango ya samu dama, ba shi jin tsoron yin magana kan abubuwan da masu kallo ke yawan magana a kansa - aure-auren da ya yi zuwa yanzu.

Lokacin da ya samu irin wannan damar a shirin Mahangar Zamani, Zango ya bayyana manyan abubuwa biyu da suka sa abubuwa suka "cunkushe masa" a rayuwa.

Na farko, ya bayyana matsalolin da ya samu da wasu masu shirya finafinai da kuma jarumai, sai kuma maganar iyali.

"Saboda haka, waɗannan abubuwan ne suka sa komai ya hargitse min, har ma ya zama ba ni da nutsuwar yin wani abu ko tunani mai kyau. A madadin haka na ce bari na ɗauki lokaci na nutsu kafin na ci gaba da yi wa mutane abin da suke buƙata," in ji shi.

Game da ɓangaren iyali kuma, a baya mawaƙin kuma mai shirya finafinai ya taɓa cewa ba zai sake aure ba. Sai dai a wannan hirar ya ce fushi ne ya sa shi yin wannan maganar.

"Yanzu na sauka daga kan wannan [ra'ayin]. Ƙaddara ce ta sa. Na yi na rabu da ita, na sake yi na rabu da ita, wadda ma zan yi gobe zan iya rabuwa da ita."

Ya ƙara da cewa ƙaddararsa ce kuma "mutane sun kasa gane hakan", shi ya sake yawan zargin sa cewa yana auri-saki.

'Saboda wannan matsalar na bayar a kula min da shafukana na sada zumunta'

Asalin hoton, Adam A Zango

Adam Zango
Bayanan hoto, Adam Zango mawaƙi ne kuma mai shirya finafinai

Da an zaci an gama bukukuwan Ƙaramar Sallah ba tare da wasu cecekuce ba daga 'yan TikTok kamar yadda suka saba, sai ga shi sunan Adam Zango ya karaɗe shafukan zumunta.

A wani lokaci daga tsakiyar shekarar 2023 zuwa ƙarshenta, an daina ganin abubuwa masu kama da labari ko martanin da zai jawo cecekuce a shafukan tauraron, wanda ya bayyana da cewa yana sane ya bai wa kan sa hutu.

Yayin hirarsa da BBC a shirin Mahangar Zamani, Zango ya ce mutum ya samu na musamman da ke kula masa da shafukan.

"Irin waɗannan abubuwan ne da suka yi yawa sai na bai wa manajana [shafukan] ya ci gaba da kula da su, ni kuma na koma gefe saboda magana ta gaskiya ba ni da haƙuri.

"Idan mutum ya faɗi wani abu a kan rayuwata wanda ya fita daga cikin masana'antar [Kannywood] to gaskiya ba na bari, saboda mutuncina ne idan ban gyara ba babu mai gyara mani."

Me ya jawo tone-tonen a yanzu?

Tun kafin ya fara fallasa wasu abubuwan da ke tsakaninsa da makusantansa, Zango ya nuna cewa zarge-zargen da mutane ke yi masa na damun sa sosai, har ya sanar cewa zai yi tone-tonen.

Alamomi sun nuna cewa ba wai da masana'antar kannywood yake faɗa ba, yana kokawa ne kan yadda wasu abokan aikin nasa suka kasa ba shi kariya a lokacin da ake zagi ko yi masa ƙazafi a shafukan zumunta, kamar yadda ya bayyana a Instagram.

Bayan zarge-zargen da ya yi wa matansa da kuma abokan aikin nasa, Zango ya zargi sauran 'yan Kannywood da yin burus da matsalolinsa.

"Na daɗe ina faɗa muku matsalata a waƙoƙina amma kun kasa fahimta, zan ci gaba da yaƙin nema wa kaina 'yanci," kamar yadda ya wallafa a Instagram.

"An zage ni, an zagi mahaifiyata, an zagi 'ya'yana ina kallo ban yi magana ba, amma duk a cikin masana'antar Kannywood babu wanda ke iya kare ni sai Allah," in ji shi cikin wani bidiyo da ya taɓa wallafawa.

"Amma sai ku ['yan Kannywood] dinga biyo ni a gefe kuna cewa kada na yi magana wai ba girmana ba ne. To daga yau kada wani ya ƙara faɗa mani cewa ba girmana ba ne."

Rayuwar Adam A Zano a taƙaice

Asalin hoton, Adam A Zango

Adam Zango
Bayanan hoto, Fim ɗin Adam Zango na farko shi ne Sirfani
  • An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
  • Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
  • Ya koma rayuwa a jihar Plateau, inda ya yi karatun firamare
  • Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan lokacin
  • Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa
  • Ya koma Kano, inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
  • Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
  • Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara fiye da 20
People are also reading