Home Back

Kotu ta Yanke Hukunci kan Rikicin Sarautar Kano, An Soke Dokar Rusa Masarautu

legit.ng 2024/7/5
  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta ta yanke hukunci kan dambarwar masarautar Kano tun bayan rushe masarautun jihar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi
  • Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman a hukuncin da ya zartar a yau ya soke dokar da ta rushe masarautun Kamo, sannnan ta yi umarnin kowa ya tsaya a matsayinsa
  • Wannan na nufin Aminu Ado Bayero ya dawo karagarsa, sannan sauran masarautun na nan da sarkunansu kamar yadda suke gabanin rushe shu da gwamnati ta yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yi watsi da dokar da majalisar dokokin Kano ta yi amfani da ita wajen nada sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16.

Wannan na nufin kotun ta haramta rushe masarautun Kano da gwamnatin Abdullai Umar Ganduje ta kirkira bayan tumbuke sarki Sanusi.

Masarauta
Kotu ta yanke hukunci kan sarautar Kano Hoto: Masarautar Kano Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta majalisar dokokin jihar ta mayar da sarki Sanusi II kujerarsa tare da sauke sarakunan da Ganduje a nada a shekarar 2020.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basarake ya shigar da kara kotu

Tun bayan tunbuke sarki Aminu Ado Bayero na Kano, da sauran sarakunan Kano, basarake kuma daya daga masu nada sarki Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da kara kotu, Justice watch News ta wallafa.

Dan Agundi na karar gwamnatin Kano na rushe masarautar Kano wanda ya ce an keta masa ‘yancinsa na dan Adam, kamar yadda lauyansa, Chikaosolu Ojukwu (SAN) ya shaidawa kotun.

A hukuncin da ya yanke a yau, mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya yi watsi da dokar gwamnatin Kano, wanda ke nufin har yanzu Aminu Ado Bayero shi ne halastaccen sarki.

Umarnin kotun da ta rushe dokar tsige sarakunan Kano na nufin sarakunan Bichi, Karaye da Gaya na nan kan karagarsu, tare da tumbuke Sanusi II.

Kotu ta magantu kan shari'ar masarauta

A wani labarin kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman ta magantu kan sahihancin dokar rushe masarautu,

Magatakardar kotun ya shaidawa lauyoyin bangarorin biyu cewa mai shari'a Muhammad Abdullahi Liman ya dage zaman kotun zuwa karfe 2:00 na rana.

Asali: Legit.ng

People are also reading