Sarautar Kano: NNPP Ta Yi Hannu Riga da Kwankwaso Kan Zargin Tasa Tinubu a Gaba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta barranta kanta da zargin rubuta wasika da Rabiu Kwankwaso ya yi ga ƴan Majalisunta na Tarayya.
Jam'iyyar ta ce Kwankwaso ya rubuta wasika ga mambobin domin sukar Bola Tinubu kan dambarwar sarautar Kano.
NNPP a cikin wata sanarwa ga Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ta ce ba da yawunta Kwankwaso ya yi hakan ba, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata kungiya ce ta bankado cewa Sanata Kwankwaso ya rubuta takarda inda yake umartar mambobin Majalisar na NNPP su tasa Tinubu a gaba kan zargin hannu a rigimar sarauta.
Shugaba jam'iyyar, Agbo Gilbert da sakatarensa, Kwamred Oginni Olaposi Sunday sun bukaci Majalisar ta yi watsi da umarnin Kwankwaso, Leadership ta tattaro.
"Mun samu labarin wata takarda da ke yawo da saka hannun Dakta Ajuji Ahmed da aka rubuta ga Majalisar Tarayya."
"Muna son tabbatar da cewa wasikar da Dakta Ajuji ya rubuta ba ta da alaka da jam'iyyar NNPP kuma ba tare da sahalewarta ba ne."
"Kan maganar rigimar masarautu, lamarin yana gaban kotu kuma tsoma bakin Majalisar kawai kara ruruta wutar rikicin zai yi."
- Jam'iyyar NNPP
Jam'iyyar ta kara da cewa ta himmatu wurin tabbatar da kawo ci gaba a Najeriya da inganta rayuwar al'ummar kasar.
Kun ji cewa wata kungiya mai suna Progressives League of Youth Voters ta zargi Rabiu Kwankwaso da rubuta wasika ga ƴan Majalisa kan rigimar sarauta.
Ana zargin Sanatan ya rubuta takarda ne domin umartan mambobin NNPP su tasa Bola Tinubu a gaba kan zargi hannu a rigimar sarautar jihar.
Asali: Legit.ng