Home Back

Muna samun hadin kai dari bisa dari daga majalisar dokokin jihar kano:Engr Abba Kabir Yusif.

dalafmkano.com 2024/5/11

Gwamnatin jihar kano ta ce tana samun hadin kai dari bisa dari daga majalisar dokokin jihar kano.

Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusif ne ya bayyana hakan yayin taron walimar buda da ya jagoranta a daren Litinin din nan tare da yan majalisun dokokin jihar kano, da kuma yan majalisun dake wakiltar jihar kano a zauren majalisar dokoki ta kasa.

Engr Abba Kabir Yusif ya ce yana fatan wannan hadin kan da yake samu zai dore domin cigaba da hidimtawa al’ummar jihar kano kamar yadda sukayi alkawari yayin yakin neman zabe na shakarar 2023 da ta gabata.

Gwamnan ya kara da cewa sakamakon aikace – aikacen da al’ummar kudancin kasar nan ke samu ta bangaren babban dan kasuwar nan dan asalin jihar kano Alhaji Aliko Dangote, hakan tasa gwamnatin ta hada guiwa dashi domin itama kano ta amfana da irin wa’yannan ayyukan, inda yace nan bada jimawa za’ayi manyan titina guda biyu a jihar kano karkashin kulawar Aliko Dangote.

Daga bisani yayi kira ga ‘yan majalisun tarayya dasu kara kaimi wajen samowa jihar kano manyan ayyukan cigaba, kamar yadda wakilinmu na fadar Gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito mana.

People are also reading