Home Back

Ministan Tinubu Ya Koka Kan Yadda Ake Gudunsa Bayan Taimakon Wasu a Zaben 2023

legit.ng 2024/7/7
  • Ministan ayyuka, Dave Umahi ya yi martani kan yadda ƴan siyasa ke cin amanar iyayen gidansu wadanda suka taimake su a rayuwa
  • Umahi ya bayyana cewa akwai wadanda ya taimake su a zaben da aka gudanar a 2023 suka hau madafun iko amma yanzu suna gudunsa
  • Ministan ya bayyana haka a birnin Abakaliki da ke jihar Ebonyi a yau Alhamis 30 ga watan Mayun da muke ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ebonyi - Ministan ayyuka a Najeriya, Dave Umahi ya koka kan yadda ake cin amana a siyasa.

Umahi ya ce mafi yawan wadanda ya taimake su suka samu mulki a zaben 2023 yanzu gudunsa suke yi.

Ministan Tinubu ya magantu kan cin amanarsa da aka yi a siyasa
Ministan ayyuka, Dave Umahi ya koka kan yadda ake cin amana a siyasa. Hoto: @realdaveumahi. Asali: Twitter

Umahi ya ce yaransa suna gudunsa

Ministan ya bayyana haka ne a yau Alhamis 30 ga watan Mayu a birnin Abuja da ke jihar Ebonyi, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce hatta mambobin Majalisar Tarayya da ya taimakawa suna gudunsa yanzu sai dai ta ce ko a jikinsa bai damu ba, Punch ta tattaro.

"Cif Onyekachi Nwebonyi ne kadai zai iya kira na mai gidansa, amma sauran sun tsoron gwamna zai yi fushi da su."
"Gwamnan ba zai yi haka saboda shi ma sa kansa yana fada nine sanadin nasararsa a cin zabe."

- Dave Umahi

Babu lokacin yaki da Nwifuru - Umahi

Umahi ya ce zai yaki duk wanda ke neman fada da gwamnan jihar saboda ya cancanci mutuntawa daga gare su.

Ministan ya ce kamar yadda ake samun matsala tsakanin gwamna da mai gidansa shi ba shi da wannan lokaci a yanzu.

Kotu ta hana Alia binciken Ortom

A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun jiha da ke Makurdi ta dakatar da Gwamna Alia Hyacinth binciken tsohom gwamna, Samuel Ortom.

Kotun ta ce akwai korafi da Ortom ya shigar wanda ke buƙatar daukar mataki kafin ba da bahasi kan binciken.

Wannan na zuwa ne bayan Hyacinth ya kaddamar da kwamitin bincike guda biyu a watan Faburairu kan tsohon gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading