Home Back

Ganawar Siyasar Kwankwaso Da el-Rufai A Sikeli

leadership.ng 2024/8/23
kwankwaso

Tun bayan da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufa’I ziyara a gidansa da ke Abuja, jama’a suke ta fadin albarkacin bakinsu kan wannan ganawar na jiga-jigan ‘yan siyasa, wanda sanin kowa ne ganawar tana da alaka da tunkarar zaben 2027, domin kuwa su kansu ‘yan siyasa sun sana cewa, ‘sai an hada karfi da karfe sannan za a kai ga gaci.

Kwankwaso da el-Rufai suna da kamanceceniya a wasu abubuwa guda 10 da suka hada da:
Dukkanninsu dai sun yi gwamna na shekara takwas-takwas a jihohinsu kuma sun rike mukamin minista na zango, inda Kwankwaso ya yi ministan tsaro, yayin da el-Rufai ya yi ministan Babban Birnin Tarayya Abuja.
Haka kuma dukkaninsu sun nada magadansu a lokacin da za su bar mukamin gwamna a jihohinsu, kuma daga baya wadannan magadan nasu suka butulce masu suka koma abokannin adawarsu.

Kazalika, dukkanin suna amfani da ikon da suke da shi wajen danne kowa, hakan ya sanya ake yi wa kowa lakabi da karfin ikon da yake da shi. Inda ake yi wa Kwankwaso lakabi da ‘DanMusa mai takalmin karfe, kowa ka taka ya taku,’ shi kuma el-Rufai ake yi masa lakabi da ‘Mai Rusau’.

Sannan kuma dukkansu an zarge su da badakkala da kudaden gwamnati a lokacin da suke madafun iko, inda aka rika sa-toka, sa-katsi tsakaninsu da hukumomin yaki da rashawa.

Dukkansu sun taka muhimmiyar rawa wajen bai wa jam’iyyar gwamnati damar yin nasara a zaben 2023, inda Kwankwaso ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, yayin da el-Rufai kuma ya yi ruwa ya yi tsaki wajen tallata kudirin takarar musulmi da musulmi a yankin arewa har aka kai gaci, wato jam’iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Kwankwaso da el-Rufai sun nuna ra’ayinsu na zama shugaban kasa wanda suka nuna kwadayinsu a kan yankin arewa, domin idan sun sami nasara a arewa sun rage aiki.
Dukkaninsu kyankyasar jam’iyyar PDP ne wadanda suka bar jam’iyyar, a yanzu kuma suke son angulu ta koma gidanta na tsamiya.

Haka kuma dukkaninsu sun so su yi aiki a cikin gwamnatin Tinubu, amma ba su sami dama ba.
Kwankwaso da el-Rufai dukkansu dai barazanar siyasa ne ga Shugaban kasa Bola Tinubu, inda za su iya kasancewa masu adawa mai karfi da zai kawo karshen tuninsa na zarcewa a kan karagar mulki karo na biyu da Tinubu ke muradi.

Lallai wadannan jiga-jigan siyasar suna bukatar junansu duk da irin bambance-bambancen da ke tsakaninsu wajen cimma muradinsu a siyasance. Don ko a falsafar siyasa ana cewa ‘abokin adawa, abokin hamayyata, abokina ne’.

A bangare guda kuma, shugaban kungiyar ci gaba matasa (AYCF), Yerima Shettima ya bayyana cewa ganawar Kwankwaso da el-Rufai makarkashiya ce ga mulkin Tinubu.

Shettima ya nuna fargabarsa kan ganawar Kwankwaso da el-Rufai ne a lokacin da yake zantawa da Jaridar LEADERSHIP a karshen mako.

Da yake tabbatar da ganawar, Kwankwaso a cikin sakonsa na kafar sada zumunta ta Tuwita ya ce, “Ina son in kai ziyarar gaisuwa ga tsohon abokin aikina, H.E Nasir el-Rufai, a gidansa da ke Abuja a yau.”
Har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan tattaunawar tasu ba, amma wata majiya da ke kusa da su ta yi nuni da cewa, ganawar ta kasance wani bangare ne na gina tsohuwar alaka da kawance da ka iya kaiwa ga kawancen siyasa gabanin babban zaben 2027.

Sai dai wani jigo a jam’iyyar APC, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ganawar ba wani abu ba ne illa taron mutanen da aka fusata, na neman su dawo da martabarsu.

Wannan ita ce ganawa ta farko a tsakanin el-Rufai wanda ya kasance nag aba-gaba wajen yakin neman zaben Tinubu a 2023 da Kwankwaso wanda ya zo na hudu a zaben tun bayan a aka kammala zaben shugaban kasan.

Duk da cewa el-Rufai ya ci gaba da zama jigo a jam’iyyar APC, tun bayan da ya rasa samun mukamin minista bayan majalisar dattawa ta ki amincewa da nadin nasa.

Yanzu haka dai el-Rufai da Kwankwaso na ci gaba da fuskantar rikicin siyasa a jihohinsu.
Kwankwaso na fuskantar rikicin da ya barke kan kujerar Sarkin Kano da kuma tuhumar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje, ya kara dagula lissafi, tsakanin Kwankwaso jagoran jam’iyyar NNPP ta Kano da Ganduje shugaban APC na kasa.

A Kaduna kuwa, rashin jituwar da ke tsakanin el-Rufai da Gwamna Uba Sani, wanda ya gada shi kuma yaronsa a siyasa, ya kai ga tuhumi tsohon gwamnan da majalisar dokokin Jihar Kaduna ta yi a kan zargin karkatar da naira biliyan 432, zargin da el-Rufai ya kalubalanta a gaban kotu.

People are also reading