Home Back

Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani

leadership.ng 2024/7/3
Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani
World Bank on glass building. Mirrored sky and city modern facade. Global capital, business, finance, economy, banking and money concept 3D rendering animation.

Gwamnatin tarayya da Cibiyar Aikin Noma (IITA) da Bankin Duniya da kuma sauran masu ruwa da tsaki a fannin aikin no-ma, sun ayyana kudirinsu na yin hadaka mai karfi a kan aikin noma wanda ke tattare da fasahar zamani.

Sun ayyana yin hakan ne, domin kawo karshen matsalar rashin amfani da fasahar zamani a fadin wannan kasa da kuma Na-hiyar Afirka baki-daya.

Har ila yau, wannan kuduri na kunshe ne sakamakon wata ganawa da a aka yi tsakanin Mataimakin Shugaban Kasa, Sana-ta Kashim Shettima da wata tawaga da ta zo daga Cibiyar IITA da Bankin Duniya da kuma Cibiyar Gudanar da Bincken Tsarin Abinci ta Kasa da Kasa (IFPRI).

Kazalika, Mataimakin Shugaban Kasar; a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha ya fitar ya ce; an yi wannan ganawa ce, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Jawabin Shettima a wajen ganawar ya bayyana cewa, shirin zai mayar da hankali ne kan yadda za a kara samar da wadataccen abinci a fadin kasar nan baki-daya.

Mataimakin ya ce, Cibiyar IITA ta kai matsayin da za ta taimaka wa ba Nijeriya kadai ba, har da ma dukkanin daukacin Nahiyar Afirka, ta yadda za a kara saita tsarin aikin noma da zai iya ju-rewa kowane irin sauyin yanayi tare da kara inganta Irin noma.

Haka zalika, ya yi nuni da cewa; Cibiyar IITA wadda aka kafa ta a shekarar 1967, ta jima tana bayar da gudunmawa ga wannan fanni na aikin noma a Nijeriya, sannan ya kara da cewa; har yanzu muna bukatar wannan gudunmawa tata.

Kazalika, Shettima ya sanar da cewa; nan da 2050, Nijeriya za ta kasance kasa ta uku cikin mafi yawan al’umma a doron kasa.

Ya sanar da cewa, Nahiyar Afirka na fusakantar kalubalen fari, sauyin yanayi da kuma kalubalen rashin tsaro, inda ya kara da cewa, fannin aikin noma na kasar nan na matukar fusakantar koma baya.
Har wa yau, Shettima ya yi kira ga Cibiyar ta IITA, da ta karfafa wannan hadaka, musamman domin samun damar zuba jari a fannin aikin noma ta fuskar kasuwanci.

Sannan kuma, ya bukaci cibiyar ta taimaka wa Nijeriya da ingantaccen Irin shuka na Masara da sauran amfanin gona, musamman Rogo.

Daga nan kuma, ya yaba wa IITA kan yunkurinta na samar da ingantaccen Irin Rogo a yankin kudu maso yamma, inda ya nemi cibiyar da ta kara fadada wannan shiri zuwa sauran kasashen da ke Nahiyar Afirka.
Tun da farko a nasa jawabin, Darakta Janar na Cibiyar IITA, Dakta Simeon Ehui, gode wa Shettima ya yi a kan shugabancinsa da kuma yadda ya mayar da hankali wajen bunkasa fannin aikin noma na kasar nan da kuma goyon bayan da yake bai wa cibiyar.

Dakta Ehui ya kara da cewa, tawagar ta zo Abuja ne; domin ganawa musamman a kan yadda za a sabunta yin hadaka da cibiyar da kuma sauran masu ruwa da tsaki, bisa nufin taimaka wa gwamnain tarayya na kokarinta wajen samar da wadatac-cen abinci a Nijeriya da kuma Nahiyar Afrika baki-daya.

Shi ma a nasa bangaren, Mataimakin Darakta Janar na IITA; Dakta Dashiell Kenton ya bayyana cewa, wannan cibiya tasu na taimaka wa wasu shirye-shiryen gwamnatin tarayya a fannin aikin noma, domin samar da damar kirkiro da wasu ayyukan yi, musamman ga matasan Nijeriya.

Haka zalika, ya yaba da fannin shirin noma don samun riba; wanda Gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Tinubu ta kirkiro da shi, wanda ya yi nuni da cewa; shirin zai sake karfafa guiwar matasan kasar nan da dama.

Kazalika ya sanar da cewa, ta hanyar wannan shiri; cibiyar za ta tallafa wa manoman wannan kasa, musamman kanana ta hanyar ilimatar da su kan yadda za su bunkasa nomansu.

A nasa jawabin, Manajan Sashen Noma da Samar da Abinci na Bankin Duniya, Mista Abel Lufafa ya bayyana cewa, bankin da IITA da sauran masu hadaka; sun ji dadi da irin gudunmawar da Gwamnatin Shugaba Tinubu ke bayarwa, wajen kara habaka fannin aikin noma na Nijeriya.

People are also reading