Home Back

An Ɗage Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Bauchi

leadership.ng 2024/10/5
An Ɗage Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Bauchi

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BASIEC) ta sanar da sauya ranar da za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, inda ta ɗaga shi daga ranar 10 ga watan Agusta zuwa 15 ga watan Agusta, 2024. Shugaban Hukumar, Ahmed Makama ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

Makama ya bayyana cewa an ɗaga ranar zaɓen ne saboda wasu dalilai da suka wuce ikon hukumar. Ya kuma buƙaci dukkan jam’iyyun siyasa, da masu ruwa da tsaki, da kuma sauran jama’a da su lura da wannan sauyin tare da ba su haƙurin duk wani rashin jin dadi da sake jadawalin zaɓen ya haifar.

People are also reading