Home Back

Gwamnatin Tarayya ta yi Barazanar Kwace wasu Lasisin Rijiyoyin Mai

legit.ng 2024/5/18
  • Gwamnatin tarayya ta yi barazanar kwace lasisin da ta bawa wasu daidaikun jama'a da kamfanonin da ba sa kawowa kasar nan haraji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar da kwace lasisin rijiyoyin mai da ba a amfani da su daga hannun kamfanoni da daidaikun mutane saboda rashin samun kudin shiga.

Karamin ministan ma’adanan man fetur, Heineken Lokpobiri ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a jihar Legas a wani taro da Petroleum Club ta shirya.

Asiwaju Bola Tinubu
Gwamnatin Tarayya ta yi Barazanar Kwace wasu Lasisin Rijiyoyin Mai Hoto: Asiwaju Bola Tinubu Asali: Facebook

A cewar Heineken Lokpobiri, kasar nan ta yi asarar dala biliyan 30 a cikin shekaru biyu da rabin da suka gabata, kamar yadda Punch Newspapers ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin a damuwa da asarar man fetur

Ministan ya kara da bayyana damuwar yadda masu rike da lasisin kuma ba sa hako man fetur din da cewa suna janyowa Najeriya asara.

Heineken Lokpobiri ya kara da cewa dambarwar Seplat/ExxonMobil yana janyowa gwamnatin tarayya asarar gangar mai 480,000.

Sai dai ya bayyana fatan idan gyara dukkanin matatun man fetur din kasar nan domin bunkasa tace man a cikin gida.

“ Ina sa ran gyara matatun manmu dake Port Harcourt a Warri, da na Kaduna. Yanzu da matatar man Dangote ke tasowa, da kuma wasu kananan matatun mai da muka bawa lasisi (a shirye na kara bayar da wasu), za mu iya tace man da muka sha ba wai a Najeriya kawai ba har baki dayan yankin Afrika ta yamma.”

Ana gyaran matatar man Kaduna, Minista

A shekarar 2023 ne gwamnatin tarayya ta ce ana aiki gadan-gadan domin kammala gyaran matatar man dake jihar Kaduna domin fara tace gurbataccen mai a cikin kasar nan.

Karamin ministan albarkatun mai a kasar, Heineken Lokpobiri ya ba da tabbacin bayan kai ziyarar gani da ido kan aikin matatar a karshen shekarar 2024.

Ya ce matatar man ta zamani za ta taka muhimmiyar rawa wajen rage matsalar man fetur a kasar nan idan ta kammala.

Asali: Legit.ng

People are also reading