Home Back

Champions League: Bayern Munich Da Real Madrid Sun Tashi Canjaras

leadership.ng 2024/5/18
Champions League: Bayern Munich Da Real Madrid Sun Tashi Canjaras 

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da Real Madrid sun tashi 2 da 2 a wasan gasar zakarun turai (Champions League) da suka buga a filin wasa na Allianz Arena.

Munich ta karbi bakunci Madrid ne a daren ranar Talata, a wasan kusa da na karshe na gasar.

Dan wasan gaban Real Madrid, Vinicius Junior ne ya fara jefa kwallo a minti ma 24 da fara wasan.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Bayern ta farke kwallon ta hannun dan wasanta Sane, sannan ta kara kwallo ta hannun Harry Kane a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

A minti na 83 Vinicius Junior ya warware kwallon da Munich a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Kungiyoyin biyu za su sake karawa a ranar Laraba a mako mai zuwa a gidan Real Madrid.

People are also reading