Kwankwaso Ya ba Abokin Takararsa a NNPP Mamaki a Bikin Babbar Sallah a Kano
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano- Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Bishof Isaac Idahosa ya yaba da yadda ya ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke mu’amalantar jama’a.
Bishof Idahosa ya bayyana haka ne bayan ganin yadda magoya baya su ka tarbi Sanata Kwankwaso yayin bikin sallah babba a Kano.
Leadership News ta wallafa cewa tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasar na ganin irin wannan alaka mai karfi na nuni da shugabanci na gari da jan jama’a a jika daga shugaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Bishof Isaac Idahosa ya shawarci shugabanni a Najeriya su yi kokarin gina ingantacciyar alaka mai kwari da takalawansu.
Ya bayyana haka ne bayan dandazon magoya bayan darikar siyasar kwankwasiyya sun taya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagoyar sallah babba a gidansa da ke Kano.
Daily Trust ta wallafa cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya gudanar da taron sallah a gidansa da ke Miller road inda ya samu halartar daruruwan magoya baya daga ciki da wajen jihar.
A wani labarin kun ji cewa jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima ya gargadi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan illar da jagoran kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso zai iya yiwa siyasarsa.
Buba Galadima ya fadi ra’ayinsa ne yayin da ake dambarwar masarautar Kano, kuma ya na ganin idan Tinubu bai bi siyasar Kano a hankali ba, zai lalata damarsa ta sake zama shugaban kasa.
Asali: Legit.ng