El-Rufai: Tsohon Kakakin Majalisar Kaduna Ya Shiga Matsala, Ya Faɗi Gaskiya Kan Bashin $350m
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Tsohon kakakin Majalisar jihar Kaduna, Yusuf Zailani ya yi martani kan zargin amincewa da bashin $350m.
Zailani ya ƙaryata amincewa da makudan kudi ga tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai na bashin Bankin Duniya.
Wanann ya biyo bayan kafa kwamitin bincike kan gwamnatin El-Rufai daga shekarar 2015 zuwa 2023 da Majalisar ta yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya ke kare kansa, tsohon kakakin Majalisar ya ce bai amince da bashin ba yayin da ya ke shugabancin Majalisar.
Hadimin kakakin Majalisar, Suraj Bamalli shi ya wallafa faifan bidiyo inda Zailani ke kare kansa a Majalisar Nijar.
"Na dade ina jiran wannan rana, wasu mambobin Majalisar suna wurin, shida daga cikinsu har yanzu mambobin wannan Majalisar ce."
"Cikinsu har da tsohon mataimakin shugaban Majalisar, Isaac Auta Zankhai, sun ce na amince da bashin amma na naƙi, na ce ya kamata mu san bashin nawa muke da shi."
- Yusuf Zailani
Majalisar ta kuma bukaci a gayyato tsoffin kakakin Majalisar na takwas da kuma na da tsohon kwamishinan kudi.
Sauran sun hada da daraktoci a ma'aikatu da kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare da sauran masu da riƙe da manyan mukamai.
A wani labarin, Majalisar jihar Kaduna ta tura sakon gargadi ga ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bello El-Rufai.
Majalisar na zargin Bello da tura mata sakon barazana da kuma kakakin Majalisar, Yusuf Liman kan binciken da Majalisar ta kafa kan Nasir El-Rufai.
Hakan ya biyo bayan zargin da Gwamna Uba Sani ya yi kan tulin bashi da tsohon gwamnan ya bar masa a gwamnanti.
Asali: Legit.ng