Home Back

An Shiga Jimami Bayan Mutum 116 Sun Rasu a Wurin Taron Addini

legit.ng 2 days ago
  • Aƙalla mutane 116 ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da ya auku a wajen wani taron addini a Arewacin ƙasar Indiya
  • Mutanen da suka rasa ransu sakamakon turmutsitsin wanda ya auku a ranar Talata sun haɗa da mata masu yawan gaske da wasu yara
  • An yaɗa wasu bidiyoyin da ba a tantance su ba a shafukan sada zumunta inda suka nuna gawarwaki jibge a gaban wani asibiti

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Hathras, Indiya - Mummunan turmutsitsin da ya auku a tsakanin dubban mutane a wani taron addini a ƙasar Indiya ya jawo asarar rayukan mutum 116.

Lamarin wanda ya auku a Arewacin Indiya ya kuma yi sanadiyyar jikkata wasu mutane da dama.

Mutane sun mutu a wajen taron addini a Indiya
Turmutsitsi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a Indiya Hoto: STR Asali: Getty Images

Mutane da dama sun rasu a Indiya

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito a ranar Talata 2 ga watan Yuli, mata da yara da dama na daga cikin waɗanda suka mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jaridar Aljazeera, jama'a da dama ne suka taru a wani ƙauye da ke gundumar Hathras na jihar Uttar Pradesh domin sauraron huɗubar wani malami.

Sai dai wata iska mai tsananin ƙura da ta tashi a wurin ta haifar da firgici a lokacin da mutane ke ƙoƙarin fita.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Ashish Kumar, mai kula da gundumar Hathras, ya bayyanawa manema labarai yadda lamarin ya auku.

"Lamarin ya faru ne saboda cunkoso a lokacin da mutane ke ƙoƙarin barin wurin."

- Ashish Kumar

'Yan sanda sun ce mutane rututu rasu

Babban jami’in ƴan sanda a jihar Uttar Pradesh, Shalabh Mathur, ya tabbatar da cewa mutane 105 sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu mutum 84 suka samu raunuka kuma an kwantar da su a asibitoci.

Bidiyoyin da ba a tantance ba a shafukan sada zumunta sun nuna wasu gawarwaki da aka jibge a gaban wani asibitin yankin.

An rushe masallaci a Indiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Indiya ta rushe wani masallacin Juma’a wanda ya kai aƙalla shekara 600 mai cike da tarihi a birnin New Delhi da ke ƙasar.

Rushe masallacin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gangami kan a rushe masallata domin maye gurbinsu da wuraren bautar addinin Hindu.

Asali: Legit.ng

People are also reading