An Shiga Jimami Bayan Mutum 116 Sun Rasu a Wurin Taron Addini
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Hathras, Indiya - Mummunan turmutsitsin da ya auku a tsakanin dubban mutane a wani taron addini a ƙasar Indiya ya jawo asarar rayukan mutum 116.
Lamarin wanda ya auku a Arewacin Indiya ya kuma yi sanadiyyar jikkata wasu mutane da dama.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito a ranar Talata 2 ga watan Yuli, mata da yara da dama na daga cikin waɗanda suka mutu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar jaridar Aljazeera, jama'a da dama ne suka taru a wani ƙauye da ke gundumar Hathras na jihar Uttar Pradesh domin sauraron huɗubar wani malami.
Sai dai wata iska mai tsananin ƙura da ta tashi a wurin ta haifar da firgici a lokacin da mutane ke ƙoƙarin fita.
Ashish Kumar, mai kula da gundumar Hathras, ya bayyanawa manema labarai yadda lamarin ya auku.
"Lamarin ya faru ne saboda cunkoso a lokacin da mutane ke ƙoƙarin barin wurin."
- Ashish Kumar
Babban jami’in ƴan sanda a jihar Uttar Pradesh, Shalabh Mathur, ya tabbatar da cewa mutane 105 sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu mutum 84 suka samu raunuka kuma an kwantar da su a asibitoci.
Bidiyoyin da ba a tantance ba a shafukan sada zumunta sun nuna wasu gawarwaki da aka jibge a gaban wani asibitin yankin.
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Indiya ta rushe wani masallacin Juma’a wanda ya kai aƙalla shekara 600 mai cike da tarihi a birnin New Delhi da ke ƙasar.
Rushe masallacin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gangami kan a rushe masallata domin maye gurbinsu da wuraren bautar addinin Hindu.
Asali: Legit.ng