Karshen 'Yan Bindiga Ya Zo, Gwamna Ya Shirya Sanya Hannu a Wata Doka, Ya Yi Gargadi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya ce ba zai yi wata-wata ba domin kawo karshen 'yan yadda a jijar.
Kwamred Nasir ya ce zai tabbatar da dokar da za ta ayyana kisa kan duk masu ba 'yan bindiga bayanai a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin jaje a kauyen Tudun Bichi a karamar hukumar Danko-Wasagu kan hare-haren 'yan bindiga, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi alkawarin ba jami'an tsaro dukkan goyon baya domin tabbatar da samun nasara a dakile 'yan ta'addan, cewar Daily Post.
"Ayyukan masu ba 'yan bindiga bayanan sirri ya saba tsarin al'adu har ma da addini."
"Wasu marasa tausayi kawai za su dauki bayanai masu muhimmanci su ba 'yan bindiga domin kai hare-hare ga bayin Allah."
"Ba zan taba barin haka ya ci gaba da faruwa ba, masu irin wanna hali su sani idan aka kama su, zan dabbaka dokar hukuncin kisa kansu nan take."
- Nasir Idris
Dagacin kauyen Tudun Bichi, Muhammad Mika'ilu ya godewa gwamnan kan wannan ziyara da ya kawo musu.
Mikailu ya ce hare-haren da bindiga ya hana su yin noma kusan shekaru biyu kenan a ƙauyen.
Ya bukaci Gwamna da ya taimaka a karo musu jami'an tsaro a yankin domin samar da tsaro mai inganci.
Kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari jihar Katsina inda suka hallaka mutane 24 yayin farmakin.
Maharan sun kai harin ne a unguwar Sarkin Noma da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar a daren ranar Alhamis 2 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng