Sojoji Sun Gano Gidan Burodin ’Yan Ta’addan ISWAP a Jihar Borno
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Dakarun sojin Najeriya karkashin Operation Hadin Kai sun gano wani wuri da 'yan ta'addan ISWAP ke kera burodi a jihar Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gano gidan burodin ne a wani lungu da ke Maisani, Timbuktu Triangle a karamar hukumar Dambuwa.
A cewar jaridar the Cable, a ranar Lahadin da ta gabata wani mai fashin baki a kan harkar tsaro, Zagazola Makama, ya bada sanarwar cewa sojoji sun gano gidan burodin yayin da suka kai wani farmaki yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wasu rahotanni kuma an samu cewa gano gidan burodin ya zo ne bayana kai farmaki da sojojin suka yi na tsawon sati a maboyar 'yan ta'addan.
A cewar jaridar Punch kuma, sojojin sun yi nasarar lalata kayayyaki da dama a wurin ciki har da wurin hada burodin da sauran kayan hada shi.
'Yan ta'addan dai su ake zargi da kai hare-hare masu muni a yankunan jihohin Borno da Yobe tare da lalata wayoyin sadarwa da suka hada jihohin.
A cewar Makama, duk kuma da irin hatsarin da yankin ke da shi da irin shirin da 'yan ta'addar suka yi, sojojin sun samu nasar kutsawa da nasara a kan su.
A wani rahoton kuma, kun ji cewa sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a kan mayakan Boko Haram yayin wani arangama da suka yi a yankin Mafa da ke jihar Borno
A yayin fafatawa tsakanin sojoji da Boko Haram, dakarun Operation Hadin Kai sun halaka mayakan kungiyar ta'addancin masu yawan gaske.
Asali: Legit.ng