Home Back

Kotun Iran ta janye hukuncin kisa da aka yanke wa mawaki

dw.com 2024/7/3
Hoto: Claire Serie/BePress/ABACA/picture alliance

Kotun kolin Iran ta janye hukuncin kisan da aka yanke wa fitaccen mawakin kasar Toomaj Salehi, wanda aka daure bayan samunsa da laifin tunzura jama'a gudanar da zanga-zanga sakamakon mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun jami'an tsaron kasar.

Lauyansa Amir Raisian ne ya wallafa janye hukuncin a shafinsa na X, yana mai cewa kotun kolin ta bada umarnin sake nazartar shari'ar, sakamakon kurakuran da ta ce an tafka a shari'ar, bayan tun da farko an yanke masa hukuncin kisan a cikin watan Afirilun da ya gabata.

An dai kama mawakin mai shekaru 33 a cikin watan Oktoban shekarar 2022, bayan kazamar zanga-zangar da ta biyo bayan mutuwar matashiyar, wadda aka kama bisa laifin rashin yin lullubi.

Zanga-zangar dai ta janyo mutuwar darurun Iraniyawa ciki har da 'yan sanda.

People are also reading