Home Back

RAHOTON MUSAMMAN: Shugabannin Musulunci sun zare takubban yaƙi da gwamnatin Sokoto, kan ‘shirin ci wa Sultan mutunci’

premiumtimesng.com 2024/8/22
RAHOTON MUSAMMAN: Shugabannin Musulunci sun zare takubban yaƙi da gwamnatin Sokoto, kan ‘shirin ci wa Sultan mutunci’

PREMIUM TIMES ta tabbatar cewa shugabannin Musulunci a Najeriya sun ɗaura ɗamarar yaƙi da Gwamnatin Jihar Sokoto, tare ɗaukar alwashin cewa sun ɗauki matsaya guda ɗaya ta kare daraja da martabar Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, daga duk wata barazanar tozartawa da gwamnatin jihar za ta yi masa.

Sun ɗauki wannan matsayar a ranar 2 ga Yuli, yayin wani taro da Kwamitin Taron Gaggawa na Majalisar Ƙolin Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), inda suka jaddada “cikakken gamsuwa da miƙa wuya ga Majalisar Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya da kuma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, dangane da irin nagartaccen jagorancin da ya ke yi wa addinin Musulunci a Najeriya da ɗaukacin Musulmi baki ɗayan su.

Majiya daga wurin taron ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mambobin NSCIA sun sha alwashin yin duk wani abin da za su iya wanda ya halasta ha doka, domin su kare daraja da martabar Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, daga duk wata tozartawa da wani, wasu ko gwamnati za ta yi masa.

Kwamitin ƙarƙashin shugabancin Babban Sakataren NSCIA, Ishaq Oloyede, ya ce duk wani nauyin rashin ganin mutunci da rashin ganin darajar shugabancin NSCIA daga yanzu, to za su kalle shi a matsayin fito-na-fito da addinin Musulunci da kuma Musulman Najeriya.

PREMIUM TIMES ta ji cewa kwamitin ya na magana ne kan abin da ke faruwa dangane da dambarwa da ta kunno kai a tsakanin Gwamnatin Jihar Sokoto, kan ƙoƙarin rage ƙarfin ikon Sarkin Musulmi, lamarin da ake kallo a matsayin rashin ladabi da Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Cikin watan Jiya ne Gwamnatin Jihar Sokoto ta aika wa Majalisar Dokokin Jihar Sokoto wani ƙudiri, wanda ta ke neman a yi wa dokar haƙƙin naɗin sarakunan gargajiya da suka haɗa da hakimai, ta yadda za a karɓe ikon naɗa hakimai da iyayen ƙasa daga hannun Sarkin Musulmi zuwa hannun gwamna.

Idan Majalisa ta sa hannu, to za a ƙwace ikon naɗa masu naɗa sarki da hakimai daga hannun Sarkin Musulmi kai-tsaye, tilas sai da amincewar Gwamna.

Da yawa na cewa wannan shiri da Gwamnatin Jihar Sokoto ya ɗauko, duk sagwangwamai ne irin wanda Gwamnatin Jihar ta Sokoto ta yi a cikin 1996, ta tsige Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi a zamanin mulkin Janar Sani Abacha.

People are also reading