Home Back

An Sake Wani Mummunan Hatsarin Mota A Kano, Mutane 25 Sun Mutu, 53 Sun Jikkata

leadership.ng 4 days ago
An Sake Wani Mummunan Hatsarin Mota A Kano, Mutane 25 Sun Mutu, 53 Sun Jikkata

Wani mummunan hatsarin mota da ya afku a jihar Kano ya laƙume rayukan mutane 25 da sanyin safiyar yau Litinin bayan da wata motar tirela ta yi hatsari a gasar sama ta Dangwaro da ke kan hanyar Kano zuwa Zariya.

Motar mai ɗauke da fasinjoji 90 tare da dabbobi, babura, da buhunan masara ta kife. Hakan ya biyo bayan wani hatsari makamancin haka a ranar Juma’ar da ta gabata a ƙaramar hukumar Kura, inda wata tirela ta kutsa kai cikin masu ibada juma’a, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 14.

Kakakin hukumar kiyaye haɗɗura ta kasa (FRSC), Abdullahi Labaran, ya bayyana cewa mutane 53 ne suka samu raunuka a hatsarin, yayin da wasu 12 suka samu raunuka.

Hatsarin ya afku ne da misalin karfe 3:30 na dare, kuma an alaƙan hatsarin da gudun wuce sa’a da kuma rashin kula da direban tirelar ya yi.

A yayin aikin ceton, masu ba da agajin farko sun samu babura shida, wayoyin hannu guda goma, dabbobi, da kuma wasu ‘yan kuɗi kadan. Ba tare da ɓata lokaci ba aka garzaya da dukkan waɗanda abin ya shafa asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin kula da lafiyarsu.

Dangane da faruwar lamarin, kwamandan hukumar FRSC Ibrahim Abdullahi, ya yi gargaɗi game da mummunar dabi’a ta safarar dabbobi, da kayayyaki, da mutane a tare, inda ya jaddada cewa irin wannan abu ya saɓa wa dokar hanya da kuma jefa rayuka cikin hadari.

Ya kuma yi kira da a rika bin ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa domin kare afkuwar hatsari a hanyoyi.

People are also reading