Home Back

Mayakan Houthi sun kama wasu ma'aikatan MDD

dw.com 2024/6/18
Mayakan Houthi sun kama wasu ma'aikatan MDD
Mayakan Houthi sun kama wasu ma'aikatan MDD

Hukumomi a Yemen sun kuma tabbatar da cewa mayakan sun kama wasu ma'aikatan kungiyoyin agaj na kasa da kasa. Mayakan dai sun kai samame ne zuwa gidaje da dama da kuma ofisoshi.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka yi Allah wadai da kama jami'an. Kawo yanzu, mayakan Houthi ba su mayar da martani kan zargin ba.

A shekarar 2014 ne, mayakan Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan gwamnatin Iran suka karbe iko da babban birnin kasar Sanaa, inda suke ci gaba da iko da wasu manyan yankunan yammacin kasar.

People are also reading