Home Back

Makamin da Amurka ta bai wa Isra'ila alama ce ta goyon baya

bbc.com 2024/5/7

Asalin hoton, EPA

.
Bayanan hoto, Isra'ila ta jaddada aniyar kai hari Rafah

Duk da mako guda ana takun saka tsakaninta da Isra'ila kan yadda take gudanar da yaƙin Gaza, an ce Washington ta ba da izinin miƙa makamanta ga kawayenta na biliyoyin daloli.

Waɗannan sun haɗa da bama-bamai sama da 1,800 MK84 2,000lb (900kg) da bama-bamai 500 MK82 500lb, da kuma jiragen yaki samfurin F35A 25, in ji jaridar Washington Post da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A baya dai an danganta manyan bama-baman da hare-haren da aka kai ta sama a Gaza wanda ya haddasa asarar ɗimbin rayuka.

Washington ta ba da dala biliyan 3.8 (£3bn) a matsayin taimakon soja na shekara-shekara ga Isra'ila.

Sai dai sabon ƙunshin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Biden ke ƙara nuna damuwa game da ƙaruwar mutuwar fararen hula a Gaza da kuma kai agajin jin kai a yankin, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana gab da faɗawa cikin yunwa.

Har ila yau gwamnatin ta ce ba za ta goyi bayan wani gagarumin farmakin da Isra'ila take shirin kaiwa Rafah da ke kan iyakar Masar ba, inda ake da mutane sama da miliyan guda da suka rasa muhallansu

Ma'aikatar Harkokin Wajen Falasdinu a Ramallah ta soki Amurka kan rashin matsaya.

Asalin hoton, Reuters

.
Bayanan hoto, An sake zaman tattaunawa game da sakin ƴan Isra'ila da aka yi garkuwa da su.

Labarin miƙa makaman ya bayyana a ranar da shugaba Joe Biden ya yi magana game da "hanyar da da dama daga cikin Larabawa ƴan Amurka ke jin yakin Gaza".

Kazalika batun miƙa makaman ya sha suka sosai daga wasu jiga-jigan jam'iyyar shugaban kasar wadanda suka yi ta kiraye-kirayen a taƙaita taimakon sojojin Amurka ko kuma a sanya sharadi kan sauye-sauyen yadda Isra'ila ke gudanar da ayyukan soji.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta shaida wa BBC cewa ba ta iya tabbatar da yiwuwar mika makaman Amurka ba kafin a sanar da majalisar dokokin ƙasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya labarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Pentagon da kuma jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurka da kuma jaridar Washington Post cewa, tun da farko an amince da ƙarin jiragen yaƙin da ake aika wa Isra’ila a matsayin wani babban ƙunshin da majalisar dokokin ƙasar ta gabatar a shekarar 2008.

Kuma a shekarar da ta gabata kafin harin da ƙungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ya jawo yakin Gaza.

A lokacin da ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya je Washington a makon jiya, an ce ya ɗauki adadin jerin makaman Amurka da kasarsa ke son ƙarba cikin gaggawa.

Da yake ganawa da manyan jami'an Amurka, Mista Gallant ya jaddada buƙatar kiyaye martabar sojan ƙasarsa a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma shirye-shiryen tsananta rikici da ƙungiyar Hezbullah mai karfin fada a ji ta Lebanon.

ƙudurin da ke kira da a tsagaita buɗe wuta nan take

Bayan kada kuri'a, kakakin fadar White House John Kirby ya yi watsi da iƙirarin cewa Amurka ta sauya matsayinta, ya kuma musanta cewa a shirye take ta fara sharaɗin agaji ga Isra'ila.

"Ba wai ƙoƙarin yin amfani da wani nau'i na ƙarfin iko a nan tare da abokiyar ƙawancen mu ba, yana nufin taimaka musu su kare kansu," kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

"Har yanzu muna tare da Isra'ila, kuma muna samar da kayan aiki da makamai domin Isra'ila ta iya kare kanta daga barazanar Hamas."

A wani mataki da Amurka ta amince da shi, Isra'ila ta aike da manyan jami'an leken asiri zuwa kasashen Masar da Qatar domin sabunta shawarwarin kokarin sako mutanen da ta yi garkuwa da su a wani bangare na yarjejeniyar sulhu da Hamas.

People are also reading