Home Back

Sanusi II Vs Aminu: 'Yan Sanda Sun Kawo Cikas a Zaman Shari'ar Masarautar Kano

legit.ng 2024/10/5
  • An samu matsala a ci gaba da zaman shari'ar masarautar Kano sakamakon rashin kai sammaci ga waɗanda ake ƙara na ɗaya zuwa na biyar
  • Gwamnatin Kano ta shigar da ƙarar gaban babbar kotun jihar, ta roƙi a hana Aminu Ado da sauran sarakuna huɗu ci gaba da zama a karagar mulki
  • Sai dai bayan sauraron kowane ɓangare, mai shari'a Amina Adamu ta ƙara bayar da lokaci domin a kai takardar sammaci ga sarakunan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rashin kai takardar sammaci ga waɗanda ya kamata ya kawo tsaiko zaman shari'ar masarautar Kano a gaban babbar kotun jihar.

Kwamishinan ƴan sandan Kano, CP Usaini Gumel ne ya jawo tsaikon bayan gaza kai takardar sammacin kotu ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da sarakuna huɗu.

Sarki Sanusi da Abba, Aminu Ado Bayero.
Yan snada sun kawo cikas a ci gaba da zaman shari'ar masarautar Kano Hoto: Masarautar Kano, Abba Kabir Yusuf Asali: Twitter

Waɗanda suka shigar da karar sun haɗa da Antoni-Janar na Kano, kakakin majalisar dokoki da ita kanta majalisar dokokin jihar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buƙatar da gwamnatin Kano ta gabatar

Lauyan gwamnati, Ibrahim Isah-Wangida Esq, ya shigar da ƙorafi gaban kotun a ranar 27 ga watan Mayu, inda ya nemi a hana Aminu Ado ayyana kansa a matsayin sarki.

Ya kuma roƙi kotun ta dakatar da sauran sarakuna huɗu na Gaya, Rano, Bichi da Ƙaraye daga nuna kansu a matsayin sarakuna.

Alhaji Aminu Ado-Bayero(Kano), Nasiru Ado-Bayero (Bichi), Ibrahim Abubakar ll (Karaye), Kabiru Muhammad-Inuwa (Rano) da Aliyu Ibrahim-Gaya (Gaya), su ake ƙara a shari'ar.

Sauran waɗanda ake ƙara sun haɗa da sufetan ƴan sanda, Daraktan DSS, rundunar tsaron fararen hula NSCDC da rundunar sojojin Najeriya.

Yadda zaman shari'ar ya gudana a Kano

A zaman ci gaba da sauraron karar, lauyan IG Abdulsalam Saleh ya shaidawa kotu cewa ba a samu damar kai takardar sammaci ga waɗanda ake ƙara na 1 zuwa na 5 ba.

Ƴa ce babbar kotun tarayya ta yi umarnin hana jami'an tsaro kama waɗanda ake zargin, wanda hakan ya sa yan sanda suka gaza kai masu takardar shari'ar.

Lauyan gwamnatin ya sake miƙa bukatar kotu ta ɗage zaman domin bai wa jami'an tsaro damar kai saƙon shari'ar ga waɗanda ake ƙara.

Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta yanke cewa wannan dalilin da ƴan sanda suka dogara da shi bai kamata ya hana su kai takardar sammaci ga sarakunan ba.

Daga nan ta dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 24 ga watan Yuni, 2024.

Ado Doguwa ya samu nasara a kotu

A wani rahoton kuma dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya samu nasara a kotu a shari'arsa da gwamnatin jihar Kano kan zargin kisan kai.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta wanke Ado Doguwa daga zargin bisa dalilai na rashin hujjoji da kuma rashin cancanta, ta ci tarar gwamnatin Kano.

Asali: Legit.ng

People are also reading