Home Back

Tsakanin Kyau Da Ilimi Da Wayewa Da Arziki, Wanne Za Ku Zaba A Aure?

leadership.ng 2024/8/22

Jama’a barkanku da kasandewa tare da shafin TASKIRA, shafin daya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma cikin sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi soyayya, inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu;  Tambayoyin shafin ya fara da cewa; zabi guda cikin wadannan;

    A bangaren mata;

1)- Da a baki namijin da ba kya so amma kuma me kudi ne sosai sannan yanada mata tayu yanada yara matar tasa ma ba daya bace, sannan ba shi da wayewa irin ta zamani.

2)- Da a baki namijin da ki ke so sosai amma kuma talaka ne sosai ta yiwu ma ke za ki rika fadi-tashi wajen neman abin da za a ci, sannan yana da wayewar zamani daidai gwargwado. Wanne za ki dauka? kawo dalilai daya saka har ki ka dauka.

    A bangaren maza;

1)- Da a baka macen da ba ka so kwata-kwata amma kuma mahaifinta me kudi ne sosai irin wanda aka san da zamansa, kuma ba kyakkyaws ba ce, tana da ilimin zamani da gogewar rayuwa ba tada ilimin addini.

2)- Da a baka macen da kake so sosai, sai dai iyayenta ba su da hali sosai, ta yiwu ma kai za ka ci gaba da daukar nauyinsu, amma kyakkyawa ce sosai ba ta da wayewa irin ta zamani, kuma iliminta na boko ba wani me zurfi ba ne, sai iya ilimin addini. Wacce za ka dauka kuma me ya sa? Kawo dalilai.

3) – Idan namiji ko mace suka tsinci kansu a daya daga cikin wadannan me ya kamata su yi, ta wacce hanya za su shawo kan matsalar da ta same su, idan har sun riga da sun auri me wani hali ko dabi’a daga cikin wadannan?.

     Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:

Sunana Khadija Muhammad Sha’aban, Daga Jihar Kano:

kyau

A gaskiya idan har zai ba ni dukkanin farin cikin da zan bukata gwanda na auri wanda yake sona din ko da kuwa matansa uku ne, ni ce ta hudu, da na auri wanda zan zo kullum tunanin yadda zan yi na ciyar da kaina nake, bare ma idan ace ka haihu wannan ya fi ma tashin hankali, daga irin haka ne sai ki ga ka fada wata rayuwar ta daban wacce ba ta da kyau, musamman ma idan baka da sana’a sai ka fi daidaita, ka fara biye-biyen maza, amman shi wannan idan ba shi da wayewa, ni zan yi iya bakin kokarina wajen ganin ya zama wayayye, tunda ba shi da wani mugun hali na daban.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Daga Jihar Kano Rano:

kyau

Bana son wadda bana so, dalilina kuwa shi ne duk abin da za ta yi ba za ta taba burge ni ba, duk abin da za ta yi sannan ba zan taba samun kwanciyar hankali ba, shi kuma aure ana sone hankali ya kwanta. Gwara a bani wacce nake so gaskiya, dalilina kuwa shi ne wacce nake sonta take sona za ta bani farin ciki haka ni ma, domin ko ibada da kuma wajen abokai da wajen nema sai ka fi jinka a nutse, batun taimakon iyayenta kuwa ai aikin lada ne idan ma da hali har wadandama ba ‘yan’uwanta ba zan taimake su balle na abar kaunata ilmi da wayewa kuwa koda a gidana za ta same su in sha Allah. To ni dai na auri wacce nake so koda bata da duk abubuwan da aka zayyano zan yi kokarin samar mata da sune domin aurar wacce bana so koda za a  yanken talaucin duniya ne ba zan taba jin dadin zama da ita ba za ta iya jefa ni a halaka ko na jefa ta to, kuma bayan mutuwa akwai hisabi don haka kowa ya auri wanda yake so domin a gudu tare a tsira tare. Allah ya sa mu dace ya bar mu da masoyanmu.

Sunana Aishat Aleeshat Daga Jihar Kano:

kyau
Ni gaskiya gara na dauki namijin da bana so wanda yake da Mata da yara saboda kuwa shi na san zai bani ci da sha da sutura, sanan kuma ba ni ba fargabar yunwa, maganar matansa kuwa ai ba a kaina za su zauna ba ni ma ba a kansu zan zauna ba, tayu ma tun da mai kudi ne kowa gidan sa daban kin ga ban da matsala dasu matsalar rashin so ne, rashin so kuwa indai da kyautata wa ko ban so shi ba tabbas zan ga girmansa, zan kuma mutumta shi. Rashin wayewa kuma wannan matsalarsa ce tun da ba daurashi zan yi ina yawo da shi ba, kuma kudi zai sa ba sosai mutane ma za su lura da rashin wayewar sa ba, Allah ya sa mu dace.

Sunana Abba Usman Prado Daga Hadejia Jihar Jigawa:

kyau
Ni zan auri ‘yar mai matsakaicin karfi wadda nake so kuma take sona domin soyayyar ta da iliminta za su amfanar da ni rayuwa ingantacciya.

Sunana Hassana Hussain (Haseenan masoya), Daga Jihar Kano:

kyau
Gaskiya ni dai a nawa ra’ayin gwanda a bani saurayi koda abincin da zamuci kullum sai ya futa ya nema to, ni na fi son sa da a bani mai kudi kuma mai mata kuma mara wayewa. Dalilin da ya sa nace gwanda a bani talaka saurayi, saurayi wayayye yanada dadin zama zai rinka nuna miki soyayya da kulawa kuma kulawa ita ce aure sai ki ga kullum kina cikin farin ciki kuma wataran zai dauke ki ya kai ki wajen shakatawa duk dan ya saki farin ciki ko wannan talaucin ma ba kya dubawa sai ki ga an zauna lafiya, musamman aka ce yanada ilimin addini, sannan kuma za ki rinka yin kasuwanci kuma shi ma yana neman halal dinsa sai ki ga komai ya zama labari tunda ba abun da yake dawwamamme sai watarana ku yi kudin tare. Shi kuma namiji wanda ba wayayye ba kuma mai mata shi fa koda ya aure ki ba shida lokacinki wani ma idan ya fita tun safe sai dare zai dawo sannan kuma ba ki da wani amfani da ya wuce ki yi masa girki, sannan ya kwanta dake shi kadai ya sani, sannan hankalinshi baya kanki yana gurin ‘ya’yansa da kuma kasuwancinsa ga kuma kishin sauran matanshi da za su hana ki sakat, kuma koda wani abun ki ke yi masa na wayewa ba zai biye miki ba kila ma yayi miki kallon ‘yar iska, dan haka ni bana son irin wannan namijin.

Sunana Abdullahi Dahiru Matazu, Daga Jihar Katsina, A Karamar Hukumar Matazu:

kyau

A bangaren maza na zabi

Lamba 2 a ba ni macen da nake masifar kauna amma kuma iyayenta talakawa ne, kuma idan aka yi wani juyin ma ni zan rika daukar dawainiyar su. Dalili na shi ne; wace nake masifar kauna za ta iya zamowa silar arziki na bayan mun yi aure, za mu samu zaman lafiya mai dorewa wanda za a dade ba a ji kanmu ba. Za ta yi hakuri da duk abun da nayi mata a matsayin mai Ilimin addini, za mu samu yara dayyaba da ita. Shawara ga duk wanda ya tsinci kansa a matsayin wanda aka bashi wanda baya so ya yi hakuri ya zauna da ita ko tayi hakuri ta zauna da shi, iyayen mu ba za su so su cutar da mu ba. Allah ya kiyashemu ribatul shaidan.

Sunana Halimatu Daga Jihar Kano:

kyau
Ai dama rashin ganewa ne mu mata ke samu idon mu ya rufe mu lallai sai wanda muke bala’in so zamu aura da zarar kin je shi kuma dama naki son ya fi na shi sai abubuwa su canza, amma ni a nawa zabin gara a ba ni wanda bana so tunda yanada kudi alkhairinsa zai samar masa da soyayya ta domin an halicci zukata a bisa son wanda ya kyautata mata ne duk son da kake wa mutum idan yana kuntata maka sai ka rage wallahi matan sa kuma ba abin da ya dame ni dasu idan sun so mu zama ‘yan’uwan juna, rashin wayewarsa kuma ni zan wayar da abina daidai gwargwado.

Sunana Aminu Adamu Malam Madori A JIhar Jigawa:

To ni dai a nawa ra’ayin nafi ganin na auri wacce nake so take so na koda kuwa iyayenta masu karamin karfi ne, domin ai ita nake so ba wai abun hannun iyayenta ba, kuma ita soyayya tana gaba da komai domin koda da abun duniya a hannun iyayenta ba zai kareka da komai ba. To ni ina ganin dora soyayya a kan abun duniya kuskure ne, domin duk lokacin da abun duniyar ya kare to, soyayya ta kare don haka soyayya ta zahiri ita ce gaba da komai. Dama shi aure ibada ne ba wai sa hannun jari ba, don haka dole a fifita soyayya a gaba da abun duniya.

Sunana Lubabatu Auta Ingawa:

kyau
Zan dauki namijin da nake so talaka, dalilai na su ne; 1) Ina girmama duk abin da nake so da nuna masa muhimmanci matukar hakan bai sabawa addini da al’adata ba. 2) Zan yi kokarin kula damu da abin da nake da shi na wani lokaci. 3) Kasancewa ta ‘yar kasuwa wacce ta san dabarun kasuwanci dai-dai gwargwado zan yi amfani da wannan domin dora shi akan kasuwanci kasancewar sa me wayewar zamani cikin lokaci zai fahimci kasuwancin kuma mu hada hannu domin inganta kasuwancin da zai rike mu a gaba. 4) Halarcin da nayi masa zai sa ya rike ni da mutunci da kuma amana zan samu kyakkyawar kulawa daga garesa. 5) Ina da tabbacin ko me zai zama ba zai wulakanta ni ba saboda na zabe shi a lokacin da watakila dubunna sun gushe shi. 6) Yanada wayewar zamani ba zai hanani ci gaba da harkokin kasuwanci na ba karatu da wasu al’amurran yau da kullum. Daga karshe a daya bangaren dalili biyu ne ya hanani zaben me kudin can; Ba na sonshi, sannan ba shi da wayewar zamani.

Sunana Muhammad Najib Magaji Sansani Miga A Jihar Jigawa:

A gaskiya ni a nawa ra’ayin ina tare da Hausa da suke son maso wani koshin wahala, sannan masana suka ce “duk soyyayar bangare daya azaba ce”. Daga wannan bayanan nawa za a iya tantance ni fa ina bangaren wacce nake so domin kuwa za ta fi kulawa da ni, domin ta san ba wai wani abun ne ya sa nake zaune da ita ba sai domin Allah da kuma so da kaunar da nake yi mata. A bangare guda kuma inda ita waccen ‘yar me kudin ce koda tana sona daga abu ya shigo na sabani zai yi wuya bata yi mun gori ba, uwa uba ma gashi babu ilimin addini to, ai ‘ya’yana ma sai sun rainani domin ba za ta ji kunyar yi mun gori a gabansu ba, amma idan wacce nake so din ce duk da sabani da zai shiga tsakankani sabida iliminta na addini zai yi wuya ta walakanta ni. Ita kuma wayewa ga ‘ya mace a wannan lokaci ai ba abin so bane domin aya za ta gasa ma a hannu da sunan wayewa. A karshe ina me bawa duk wanda ya tsinci kansa a irin wannan hali shawarar yayi hakuri sannan ya mutunta abokin zamansa, sai kuma ya cika da adddu’a domin in bai yi dace ba shi/ita da farin ciki har abada.

Sunana Mansur Usman Sufi (Sarkin Marubutan Yaki), Daga Jihar Kano:

kyau

Gaskiya a nawa ra’ayin zan zabi ta biyu ne wacce iyayenta ba su da hali, kuma ba tada wayewar zaman, amma tana da ilimin addini, domin dama addini ai cewa ya yi mu zabi mai addini ba ‘yar masu hali ba. Idan fa an riga an yi auratayya a tsakanin wadannan jinsin tofa sai hakuri tare da dora juna a bisa tafarki kyakkyawa, don cimma nasara akan abin da aka sanya a gaba.

Sunana Kueen-Nasmah Daga Jihar Zamfara:

kyau

A gaskiya da a ba ni namijin da bana so me mata da yara, gaskiya gara a bani namijin da nake so a matsayin mijina koda kuwa talaka ne, koda ma a ce ni zan rika fadi tashi domin ganin na ciyar da shi, domin kuwa shi wannan talakan ban san inda Allah zai kai shi ba, shi wannan mai kudin ma ai ba da arziki aka haife shi ba, tashi yayi ya nema, saboda haka muka zamu tashi tsayi ni da nawa mijin mu nema, sannan ma  ko a bangaren matansa shi wannan mai kudi ba zai manta da matar da ta tsaya da shi da dadi da babu dadi ba, har ya kai wannan matsayin da yake, saboda haka ni ma zan tsayawa mijina duk talaucinsa, za mu tsayu kan addu’o’inmu mu fada ma Allah, da ya daukaka min mijina, kowane bawa da arzikinsa dan haka na zabi na tsaya mu yi gwagwarmaya mu shawo kan kowace matsala tare.

Sunana Haruna Garba Gidankanya, Miga, Jihar Jigawa:

kyau
To ai a nawa ganin faduwa ta zo daidai da zama muddin har ita ‘yar mai kudin za ta so ni sosai, kowa da ka gani kudi yake nema a kullum dan gudanar da harkar yau da kullum, ai da muguwar rawa gara kin tashi, kawai zan aure ta, dama kyau na dan lokaci ne kuma ba a tsufa da ilimi, za ta samu karatu mai yawa. Zan aure ta kuma za mu zauna lafiya in sha Allahu.

Sunana Muhammad Isah Zareku Miga LGA A Jihar Jigawa:

kyau
Na farko ma dukka guda biyu ba irin wace Manzon Allah (SAW) ya ce a aura ba, shi Manzon Allah cewa yayi a auri mai addini, tarbiyya, nasaba da kuma kyau din. Gaskiya gwara na auri ta biyun wacce zan ci  gaba da taimakawa iyayenta, sannan kuma na dauki dawainiyar karantarwa da ita ilimin zamani tunda tana da ilimin addini.

People are also reading