Home Back

Zargin Rashawa: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Tsohon Gwamnan Kano, Ganduje

legit.ng 2024/5/17
  • Babbar kotun jihar Kano ta ya dage sauraron shari'ar tuhumar rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
  • Kotun ta sanya ranar 16 ga watan Mayu, 2024 matsayin ranar da za ta yi hukunci kan bukatar mika takardar sammaci, ba gaba da gaba ba
  • Har yanzu dai, gwamnatin Kano ta hannun hukumar yaki da rashawa ta jihar sun gaza mika takardar sammaci ga wadanda ake tuhuma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Mai Shari’a Usman Malam Na’abba na babbar kotun jihar Kano, ya dage sauraron shari'ar tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Babbar kotun Kano ta yanke ukunci kan shari’ar Abdullahi Ganduje
Kotu ta dage shari'ar da ake yi tsakanin Abdullahi Ganduje da gwamnatin Kano. Hoto: @OfficialAPCNg Asali: Facebook

Ganduje da iyalansa da wasu makusantansa sun gurfana gaban kotun ne bisa zarginsu da karkatar da kadarorin jihar da kuma karbar rashawa, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Kotu ta dage shari’ar zuwa Mayu

Gwamnatin Kano ta hannun hukumar yaki da rashawa ta jihar ta shigar da wannan karar wadda ta jawo cece-kuce daga bangaren 'yan adawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zaman kotun na yau Litinin, 29 ga watan Afrilu, Mai Shari’a Na’abba, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Mayu, 2024.

Hukuncin ya biyo bayan sauraron bangarorin da ke shari’ar kan bukatar mika wa wadanda ake tuhumar takardar sammaci, ba gaba da gaba ba.

Tsaikon da aka samu a shari'ar

Lauyan gwamnatin Kano wanda ya ke karar su Ganduje, Barista Usman Umar Fari, ya shaidawa manema labarai cewa alkali zai bayyana matsayarsa a zama na gaba.

A ranar 17 ga watan Afrilu, Legit Hausa ta ruwaito yadda kotun ta gaza yin zamanta na farko sakamakon gaza gurfanar da wadanda ake tuhumar a shari'ar.

An tattaro cewa bangaren gwamnatin Kano sun gaza mika takardar sammaci ga Ganduje, iyalansa da wasu daga cikin wadanda ake zargin.

Gwamnatin Kano ta nemi alfarmar kotu

A kan wannan gabar ne Barista Fari ya bayyana cewa alkalin ya saurari hujjojin bangarorin biyu kan halasci ko haramcin mika sammaci ga wanda ake karar ta wata hanya daban.

A cewarsa, bangarensu sun bayyana wa alkali hujjojin da suke ganin ya halasta a bisa doka a mika wa wanda ake zargi a irin wannan shari’a sammaci ba kai tsate ba.

Sai dai an ruwaito cewa lauyoyin bangaren wadanda ake tuhuma sun soki wannan bukatar tare da cewa dole a mika sammacin kai tsaye.

Kotu ta ci tarar 'yan sanda N300m

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta ci tarar 'yan sandan Najeriya N300m kan kashe 'yan shi'a uku a Zariya.

An ruwaito cewa kotun ta nemi 'yan sandan su biya iyalan wadanda aka kashe masu yara kudin a matsayin diyya yayin da kuma ta kafa sharadi kan biyan kudin.

Asali: Legit.ng

People are also reading