Home Back

Chelsea na daf da ɗaukar matashi Guiu daga Barcelona

bbc.com 2024/7/6

Asalin hoton, Getty Images

Marc Guiu ya ci Barcelona ƙwallo biyu a kakar wasan da ta gabata
Bayanan hoto, Marc Guiu ya ci Barcelona ƙwallo biyu a kakar wasan da ta gabata

Minti 1 da ta wuce

Chelsea ta cimma yarjejeniya da baki wajen ɗaukar matashin ɗan wasan Barcelona Marc Guiu.

Ƙungiyar ta shirya tsaf wajen shirya don gwada lafiyar ɗan wasan mai shekara 18 a birnin Landan.

An fahimci cewa Barcelona ta yi yunƙurin sauya saɗarar farashin matashin da ya kai fan miliyan biyar da ke cikin kwantaraginsa ta hanyar ba shi tayin sabon kwantaragi.

Sai dai bayan mako ɗaya ana tattaunawa da wakilansa, Chelsea na daf da ɗaukar ɗan Sifaniyan mai buga wa tawagar 'yan ƙasa da shekara 19 don ƙarfafa gaban ƙungiyar.

Guiu wanda ya fito daga kwalejin koyon ƙwallo ta Barcelona, ya ci wa kulob ɗin ƙwallo daƙiƙa 23 kacal da fara buga mata wasa, inda ta doke Athletic Bilbao a 2023.

Ɗan wasan lamba tara ne mai hanzari amma kuma ba shi da ƙwarewa sosai - ya ci ƙwallo biyu cikin wasa bakwai da ya buga zuwa yanzu.

Ana ganin shi ne ɗan ƙwallo Chelsea za ta saye shi ne don buga wa babbar tawagarta wasa amma kuma ana sa ran za ta ƙaro wasu 'yan gaban a bana.

Shi ma Omari Kellyman na Aston Villa mai shekara 18 na daf da komawa Stamford Bridge ɗin kan fan miliyan 19 kan yarjejeniyar shekara biyar bayan ya kammala gwajin lafiyarsa a makon nan.

People are also reading