Home Back

Gwamnatin Tinubu za ta Binciki Yadda Buhari Ya Jinginar Filayen Jirgin Sama

legit.ng 2024/7/1
  • Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa za ta binciki yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayar da jinginar filayen jirgin sama
  • A shekarar 2023 gwamnatin tarayya ta amince a jinginar da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma Mallam Aminu Kano da ke Kano domin farfado da su
  • Amma a taron cikar shekarar Tinubu daya a kan mulki, Ministan sufurin jirgin sama, Festus Keyamo ya ce za a duba domin gano muhimman bayanai kan jinginar da su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana shirin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ya sake bibiyar jinginar da filayen saman kasar nan guda biyu da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi.

Ya bayyanawa taron masu ruwa da tsaki yayin bikin cika shekara daya na gwamnatin tarayya cewa za a sake waiwayar batun ne domin bankado gaskiyar yadda jinkinar ta kasance.

Muhammadu Buhari
Gwamnatin Tinubu za ta binciki jinginar da filayen jiragen sama Hoto: Muhammadu Buhari/ Festus Keyamo, ESQ Asali: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa ministan ya ce ba za a dukunkune jinginar filayen ba tare da bayyana gaskiyar abun da ke kunshe cikinsa ba.’

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dakatar da jirgin Nigeria,’ Keyamo

Ministan sufurin jirgin sama, Festus Keyamo ya ce gwamnati na kan bakarta na dakatar da jirgin saman Najeriya na Air Nigeria da gwamnatin Buhari ta samar a karshen mulkinta.

Ya bayyana cewa sun gano jirgin na kasar Ethiopia ne da aka makala masa tutar Najeriya wanda tsohon minister Hadi Sirika ya kaddamar.

The Guardian ta wallafa cewa tsohon minisyan ya bayyana cewa gwamnatin wancan lokaci za ta bayar da jinginar manyan filayen jirgin sama guda hudu.

Duk da a shekarar 2023, shi ma Festus Keyamo ya goyi bayan jinginar da filayen jirgin saman, amma yanzu ya ce za a sake bincikar yadda aka bayar da su jingina.

Gwamnatin ta dakatar da 'Air Nigerian'

A baya mun kawo muku labarin cewa gwamnatin tarayya ta dakatar da jirgin saman Najeriya, Nigerian Air har sai baba ta gani domin gudanar da bincike.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana cewa sun gano kura-kurai cikin yadda aka samar da jirgin, saboda haka an dakatar da shi har sai an gama dubawa.

Asali: Legit.ng

People are also reading