Home Back

Rikicin PDP: Mummunar Zanga-zanga Ta Barke a Sakatariyar Jam'iyyar, Bayanai Sun Fito

legit.ng 2024/5/18

Zanga-zanga ta barke a sakatariyar jam'iyyar PDP yayin da wata kungiya ta bukaci dakatar da Nyesom Wike kan cin dunduniyar jami'yyar da ya ke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gungun matasa sun durfafi sakatariyar jami'yya PDP a birnin Abuja yayin da ake tsaka da ganawa.

Wata kungiyar mai suna PDP Reform Vanguard ta mamaye sakatariyar inda ta bukaci a dakatar da Nyesom Wike.

Har ila yau, kungiyar ta bukaci shugaban jam'iyyar PDP, Umar Damagun da ya yi murabus daga mukaminsa.

Matasan sun dira a sakatariyar yayin da ake shirin gudanar da ganawar masu ruwa da tsakin jami'yyar, cewar rahoton Punch.

Sun zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike kan cin amanar jam'iyyar PDP wanda ya cancanci a dakatar da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading