Home Back

‘Yan Kasuwar Nijeriya Za Su Haɗa Hannu Da Gwamnatin Kaduna Wajen Bunƙasa Tattalin Arzikin Jihar

leadership.ng 3 days ago
‘Yan Kasuwar Nijeriya Za Su Haɗa Hannu Da Gwamnatin Kaduna Wajen Bunƙasa Tattalin Arzikin Jihar

Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa Ta Nijeriya ( MATAN) ta bayyana aniyarta ta haɗa Hannu da Gwamnatin Jihar Kaduna wajen bunƙasa tattalin Arzikin jihar ta bangarori daban-daban.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar, Dakta Yahaya Muhammad Kyabo Fagge a Kaduna yayin ƙaddamar da matasa ‘yan jihar Kaduna waɗanda za su yi aikin tara kuɗaɗen haraji na kasuwanni domin sauƙaƙa wa gwamnati wajen ƙara bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Shugaban ya ce ƙungiyar (MATAN) ta haɗa Hannu da Gwamnatin tarayya a kan bunƙasa tattalin Arzikin ƙasa kamar yadda Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin.

‘Mun ƙaddamar da irin wannan taro a Kudancin Nijeriya wanda yanzu ga shi mun shigo Kaduna domin ƙaddamar da shi Wanda aƙalla matasa sama da 2000 Dubu biyu za su samu aikin yi a matakai daban-daban, haka Kuma tattalin Arzikin Jihar Kaduna zai ƙara bunƙasa”

“A Nijeriya gwamnatin jihar Kaduna tana daga gwamnatoci da suka Samar da ci gaba cikin Shekara guda a bangaren ‘yan kasuwa da ilimi da Noma da sauran ɓangaren da suka shafi ci gaban Al’umma saboda haka wannan ƙungiyar tana alfahari da ta shigo Kaduna kuma ta ɗauki ‘yan Kaduna domin horas da su yadda za su taimaka wa jihar wajen bunƙasa tattalin arzikinta Baki ɗaya” inji shi.

A Nasa jawabin Shugaban kungiyar (MATAN) na Jihar Kaduna Alhaji Abdurahman Mohammed l, ya koka a kan yadda ake karɓar haraji amma baya shiga asusun gwamnati wanda a cewarsa hakan ya sanya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da kwamiti tsakanin ƙungiyar ‘yan kasuwa da hukumar tara kuɗaɗen haraji ta ƙasa domin toshe duk wata hanya da harajin gwamnati zai zurare.

Ya ce kashi 80 cikin 100 na mutanen Nijeriya ‘yan kasuwa ne, hakan ya sanya Gwamnatin Kaduna Ta ware shaguna sama da guda 300 a kasuwar bacci da za ta rabawa ‘yan kasuwa masu sana’ar gwanjo domin bunƙasa kasuwancinsu.

People are also reading