Ta'addanci: Kamar Buhari, Obasanjo Ya Samo Mafita, Ya Fadi Dalilin Matsalar Tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya fadi abin da ke kara matsalar garkuwa da mutane a Najeriya.
Obasanjo ya ce rashin aikin yi a tsakanin matasa shi ne babban dalilin ingiza matasa cikin ayyukan ta'addanci.
Tsohon shugaban ya bayyana haka a wani babban taron kasuwanci a jiya Talata 26 ga watan Maris a Legas, cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Tabbas idan muka cimma wannan burin za mu inganta bangaren tsaron Najeriya."
"Matsalar da muke samu na tsaro mata ne da matasa wadanda ba su da aikin yi, idan muka ba su aiki ayyukan ta'addanci za su ragu sosai."
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi imani da harkokin noma inda ya ce dole a mai da noma mafi muhimmanci a Najeriya.
Ya ce inganta harkokin noma ne kadai zai samar da abinci da rage yawan zaman banza da samar da kudin shiga, cewar Daily Post.
"Wani abokina ya taba ce min ni nahaukaci ne, na ce me yake nufi? Sai ya ce idan ba mahaukaci ba babu wanda zai shiga harkar noma."
"Tabbas ni mahaukaci ne kan harkar noma, idan dai a kan noma ne ka kira ni da wannan suna tabbas zan amsa."
- Olusegun Obasanjo
Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yadda zai kawo karshen matsalar tattalin arziki.
Obasanjo ya shawarci Tinubu ya nemi taimakon kasar Zimbabwe tun da sun taba shiga matsalar kuma sun wanye lafiya.
Asali: Legit.ng