Home Back

Gwamnatin Tinubu ta ƙara kuɗin wutar lantarki, yayin da talakawa ke tsakiyar gaganiyar fama da raɗaɗin tsadar rayuwa

premiumtimesng.com 2024/5/6
Ƙarin kashi 50/100 na kuɗin wutar lantarki bai shafi waɗanda ke shan wuta na awa 12 a rana ba

Gwamnatin Najeriya ta bayyana sanarwar ƙarin kuɗin wuta, kamar yadda Hukumar Raba Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar.

NERC ta ce ƙarin ya fara aiki nan take, tun daga yau Laraba, 3 ga Afrilu.

Mataimakin Shugaban Hukumar NERC, Musiliu Oseni, ya bayyana haka ne a lokacin wani taro da manema labarai, ranar Laraba, a Abuja.

Oseni ya ƙara da ruwa amma ƙarin zai shafi kashi 15 cikin kashi 100 na masu amfani da wutar lantarki, waɗanda duk da cewa su ne kashi 15, amma kuma wutar da amfani da ita ta kai kashi 40 bisa 100 na wutar ƙasar nan.

Cikin watan Janairu NERC ta ce Gwamnatin Tarayya za ta biya kuɗin tallafin wutar lantarki har Naira tiriliyan 1.6, domin sauƙaƙa kuɗin wuta cikin 2024.

Shugaban NERC, Sanusi Garba ya ce sabon tsarin ya bayyana dalla-dallar adadin kuɗaɗen da waɗanda ƙarin ya shafa za su biya.

Ya ce bisa la’akari da kuɗin tallafin da gwamnati ta ce za ta biya a cikin Janairu, ya sa ba za a ji raɗadin ƙarin kuɗin ba.

People are also reading