Home Back

Kanana Hukumomin Kano Da Jigawa 23 Na Kan Gaba Wajen Fuskantar Ambaliyar Ruwa – NEMA

leadership.ng 3 days ago
nema

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) shiyar Kano da Jigawa karkashin shugabancin Dakta Abdullahi ta bayyana hasashen na cewa kananan hukumomin Kano da Jigawa guda 23 na kan gaba wajen fuskantar ambaliyar ruwa mai karfin gaske a daminan bana.

Ta ce ambaliayar ruwa za ta iya kasancewa a daukacin kanan hukumomi Kano guda 14 ne da suka hada da Rimin Gado, Tofa, Kabo, Madobi, Garun Malam, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu, Warawa, Wudil, Sumaila, Ajingi, Kura, Dala, sai kuma kananan hukumomi 9 a Jihar Jigawa da suka hada da Ringim, Taura, Jahun, Miga, Kaugama, Auyo, Hadejia, kirikasamma, Guri.

Shugaban hukumar, Dakta Abdullahi shi ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a Jihar Kano.
Haka kuma hukumar ta ce kananan hukumomin Kano guda biyar da suka hada da Karaye, Takai, Bunkure, Dawakin Tofa, Makoda, ambaliyar ruwa bai kai na sauran kananan hukumomi 14 ba da aka bayyana.

Hukumar NEMA ta ce sauran kananan hukumomin Kano 25 da ambaliyar ruwan ba ta da karfi sun hada da Doguwa, Tudun Wada, Kibiya, Garko, Albasu, Gaya, Kiru, Rogo, Gwarzo, Shanono, Tsanyawa, Bagwai, Bichi, Ghari, Danbatta, Minjibir, Gabasawa, Gwalle, Fagge, Nassarawa, Kano Municipal, Tarauni, Ungogo, Kumbotso da kuma Gezawa.

Hukumar ta ce a Jihar Jigawa kananan hukumomi 10 da ke sahu na biyu wajen samun ambaliyar ruwa su ne, Gwaram, Dutse, Kiyawa, Kafin Hausa, Malam Madori, Birniwa, Maigatari, Gumel, Suletankarkar, Babura, sai kananan hukumomi 8 na Jigawa na kasa a barazanar samun ambaliyar ruwa mara karfi su ne, Guwa, Rona, Yankwashe, Kazaure, Garki, Gagarewa, Birnin Kudu da kuma Buji.

Shugaban hukumar, Dakta Abdullahi, ya shawarci al’umma su zama cikin taka tsantsan da kula da magunan ruwa da tsaftar mahalli da kuma yin addu’o’in samun sauki ga ambaliyar ruwan.

People are also reading