Home Back

Hajj 2024: Alhazai 600 Ƴan Ƙasa 1 Sun Mutu a Ƙasa Mai Tsarki, An Gano Abin da Ya Yi Ajalinsu

legit.ng 2024/7/3
  • Dangi da abokan arziki na ci gaba da laluben Alhazan ƙasar Masar da suka ɓara ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, 2024
  • Bayanai sun nuna cewa akalla alhazai 600 da suka fito daga Masar ne suka riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki a lokacin aikin Hajjin bana
  • Wannan alƙaluma na zuwa ne bayan jami'an kula da alhazan Masar sun sanar da cewa sun rasa mutane 323 a yayin aikin Ibada na wannan shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Makkah, Saudi Arabia - Akalla alhazan ƙasar Masar 600 ne aka tabbatar da mutuwarsu a lokacin aikin Hajjin bana 2024 a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Mutuwar alhazan na da nasaba da tsananin zafin da aka sha fama da shi wanda ya kai ma'aunin celcius 51.8 (digiri 125) a ranar Litinin, 17 ga watan Yuni.

Tsayuwar Arafah 2024.
Kasar Masar ta rasa alhazai akalla 600 a aikin Hajjin bana 2024 Hoto: Inside The Haramain Asali: Facebook

Wani jami'in diflomasiyyar Larabawa ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a ranar Laraba 19 ga watan Yuni, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, jami'in ya ce:

"Duka ƙarin mace-macen da aka samu suna da nasaba da tsananin zafin da alhazai suka fuskanta bana."

Manhajar Facebook da sauran shafukan sada zumunta sun cika da hotunan wadanda suka bata da kuma cigiyarsu ko Allah zai sa wani ya gansu.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, ‘yan uwa da abokan wani mahajjaciya ƴar kasar Masar, Ghada Mahmoud Ahmed Dawood, sun fara ciguyrsa a Facebook da sauran shafukan sada zumunta.

Sun wallafa hotunan Ghada Mahmoud tare da rokon duk Allah ya sa ya ganta ya taimaka ya tuntuɓe su. Sun ce ta ɓata tun ranar Asabar, 15 ga watan Yuni, ranar Arafah.

Wata mata da ke zaune a Saudiyya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:

"Ɗiyarta ta kira ni daga ƙasar Masar, ta nemi na taimaka na yi rubutun cigiya a Facebook ko Allah zai sa a dace. Abin farin cikin bamu ga sunanta a cikin waɗanda suka mutu ba."

A wani rahoton wani mahajjaci daga jihar Jigawa a Arewacin Najeriya ya nuna kyakkyawan hali yayin da ya tsinci jakar hannu ɗauke da maƙudan kudi a Madinah

Alhaji Abba Saadu Limawa ya yi cigiya domin bai wa mai jakar kayansa amma ba a ga mai ita ba, don haka ya kai wa hukumar NAHCON.

Asali: Legit.ng

People are also reading