Home Back

Gwamma Ya Faɗi Gaskiya Kan Zargin da Ake Na Tsige Mai Alfarma Sarkin Musulmi

legit.ng 2024/7/3

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sakkwato ta musanta zargin da MURIC ta yi na cewa tana shirin tsige mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na jihar, Sambo Bello Danchadi ya bayyana haka yayin da yake martani ranar Talata.

Ya ce gwamnatin Sakkwato ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ba ta da wani shiri na sauke Mai Alfarma Sarkin Musulmi, cewar rahoton Vanguard.

Idan baku manta ba kungiyar rajin kare haƙƙin Musulmi (MURIC) ta yi ikirarin cewa Gwamna Aliyu na shirin tuɓe Sarkin Musulmi saboda abin da ke faruwa a Kano.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin shugaban MURIC, Farfesa Isiaq Akintola ya yi gargaɗin cewa al'ummar Musulmi ba za su yarda a wulaƙanta Sultan ba.

Ya kuma nuna matuƙar damuwa kan yadda alaƙa ke ƙara tsami tsakanin gwamnatin jihar Sakkwato da fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Akintola ya ƙara da cewa rawanin Sarkin Musulmi ba na gargajiya ne kaɗai ba, inda ya yi nuni da cewa Sarkin shi ne shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar MURIC ta gargadi gwamnan Sokoto da kada ya tilastawa musulman Najeriya daukar wani mataki na daban.

Menene gaskiyar shirin tsige Sarkin Musulmi?

Da yake mayar da martani, kwamishinan yaɗa labarai na Sakkwato, Sambo Bello ya bayyana zargin da ƙungiyar a matsayin karya kuma mara tushe balle makama.

Kwamishinan ya bayyana dokar naɗi da sauke sarakunan jihar Sakkwato na nan yadda take, ba a canja ko yi mata garambawul ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading